An kama tsohon hadimin gwamna kan yada labaran karya, ya yanke jiki ya fadi a wajen gurfanar da shi

An kama tsohon hadimin gwamna kan yada labaran karya, ya yanke jiki ya fadi a wajen gurfanar da shi

  • An damke tsohon hadimin gwamna David Umahi kan harkokin yada labarai, Godfrey Chikwere bisa zargin yada labaran karya
  • A cewar rahotanni, Chikwere ya watsa wani rubutu a shafinsa na sada zumunta game da rundunar sojin Najeriya da ‘yan siyasa
  • rubutun nasa ya haifar da martani sannan kuma 'yan sanda sun cafke tsohon hadimin, inda aka gurfanar da shi a gaban kotu amma rahotanni sun ce ya fadi inda aka garzaya da shi asibiti

Jihar Ebonyi- An kama tsohon hadimin gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, Godfrey Chikwere kan zargin yada labaran karya da kalaman kiyayya.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Chikwere ya yi wani rubutu a shafinsa na Facebook cewa Sojojin Najeriya sun rasa mutuncinsu kuma ‘yan siyasa ne ke da alhakin kashe-kashe sannan kuma su ne za su baiwa iyalan wadanda abin ya shafa kudi don fara kasuwanci, a jihar.

Kara karanta wannan

NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

An kama tsohon hadimin gwamna kan yada labaran karya, ya yanke jiki ya fadi a wajen gurfanar da shi
An kama tsohon hadimin gwamna kan yada labaran karya, ya yanke jiki ya fadi a wajen gurfanar da shi Hoto: Charles Otu, Governor David Nweze Umahi
Asali: Facebook

Daga bisani wannan rubutun ya haifar da martani ta yanar gizo kuma an karanta shi akan dandamalin kafofin watsa labarai da yawa.

An ba da rahoton cewa a ranar Lahadi, 10 ga watan Oktoba, kwamishinan yada labarai da wayar da kai a jihar, Uchenna Orji, shi ne yasa aka kama shi.

Tsohon hadimin gwamnan, wanda aka fi sani da suna Baby Mouth, wanda 'yan sanda suka kama tare da tsare shi sakamakon korafin da wani jami'in gwamnatin jihar Ebonyi ya yi, ya fadi a ranar Litinin, 11 ga Oktoba, a inda ake tsare da shi, Premium Times ta rahoto.

Legit.ng ta tattaro cewa ya kamata ‘yan sanda su gurfanar da shi a gaban kotu, a ranar Litinin, amma rahotanni sun ce ya fadi a hedikwatar rundunar, sakamakon rashin lafiya.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

An rahoto cewa wanda ake zargin yana asibitin koyarwa na jami’ar tarayya ta Alex Ekwueme, Abakaliki, yana karbar magani.

Matarsa, Onyinyechi, ta tabbatar da rashin lafiyarsa ga manema labarai, a Abakaliki, a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba.

A cewarta:

“Mijina ya fara rashin lafiya, a daren Lahadi, lokacin yana ofishin‘ yan sanda. Don haka, lamarin ya kara tabarbarewa kuma asibitin 'yan sanda ba zai iya magance shi ba. Yana a AE-FETHA, tun da safe.
"Su ('yan sanda) ba su iya gano komai a asibitin' yan sandan ba amma yana cikin matsanancin rashin lafiya. Don haka, yanzu muna AE-FETHA. Daga bayanin da aka yi a ƙasa yanzu, abin da ke damun sa shine cutar Appendicitis mai tsanani. Amma ban sani ba tukuna.”

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Loveth Odah, ta ce ba ta da masaniya cewa wanda ake zargin yana AE-FUTHA, don jinya.

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekaru 60 ya kashe ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu

A martaninsa, Orji ya ce wanda ake zargin ba dan jarida bane da gwamnatin jihar ta sani ko kuma kungiyar yan jaridu ta Najeriya.

Orji ya lura cewa wanda ake zargin yana daya daga cikin wadanda ke yada labaran karya da kalaman kiyayya a fadin jihar, ya kara da cewa gwamnati na bibiyar wadanda ke aikata irin wannan aika-aikar.

Dan majalisar tarayya ke daukar nauyin Sunday Igboho da Nnamdi Kanu, Buhari ya yi ikirari

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa wani dan majalisar tarayya ne ke da alhakin daukar nauyin masu kira-kirayen neman ballewar kasar nan.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga kasar a matsayin wani bangare na bikin ranar 'yancin kai.

Ya bayyana cewa an gano hakan ne yayin da ake gudanar da bincike bayan kamun Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar neman kasar Biyafara da kuma Sunday Igboho, shugaban masu fafutukar kasar Yarbawa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan

Asali: Legit.ng

Online view pixel