Dubun wasu mutane masu kaiwa yan fashin daji kayan abinci ya cika a Abuja

Dubun wasu mutane masu kaiwa yan fashin daji kayan abinci ya cika a Abuja

  • Yan sanda sun damke wasu mutum biyu da ake zargi da aikin kaiwa yan fashin daji kayan abinci a Abuja
  • Mutanen biyu sun shiga hannun jami'an yan sanda ne yayin da suke kokarin shigar da kayan abinci yankin Kuje a cikin mota
  • Kakakin yan sanda na Abuja, DSP Adeh Josephine, ya roki mutanen Abuja su sanar da yan sanda duk wani motsi da suke zargi

Abuja - Jami'an yan sanda a babban birnin tarayya Abuja, sun damƙe wasu mutum biyu dake jigilar kayayyakin abinci zuwa Kuje a cikin mota.

Dailytrust ta rahoto cewa yan sandan na zargim mutanen da kaiwa yan fashin daji kayan abincin, yayin da suka ƙi bayyana ainihin inda zasu kai kayan.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan fashin daji dake tserowa sun fara kafa sansani a wasu yankuna na birnin tarayya Abuja.

Read also

Sojin Najeriya sun bankado farmakin da ISWAP ta kai Aulari, sun tarwatsa motocin yakinsu

Jami'an yan sanda
Dubun wasu mutane masu kaiwa yan fashin daji kayan abinci ya cika a Abuja Hoto: punchng.com
Source: UGC

Yan fashi na tilastawa mutane siyan kayan abinci

  1. Wasu daga cikin mazauna yankunan da yan fashin suka fara zama, sun bayyana cewa yan ta'addan na tilasta musu siyar da kayan abinci gare su.

Hakanan kuma yan fashin suna gargaɗin mutane kar su kuskura su faɗawa jami'an tsaro maɓoyarsu.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

A wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, ya tabbatar da cewa jami'ai sun cafke motar dake jigilar kayayyakin abinci zuwa Kuje.

Wani sashin sanarwar yace:

"Tuni jami'an yan sanda suka saka ido kan irin wannan safarar kayayyakin abincin da sauran wasu muhimman abubuwa, musamman bayan samun rahoton ayyukan masu garkuwa a Kuje."

Kakakin yan sandan ya yi kira ga mazauna Abuja su gaggauta sanar da jami'an yan sanda duk wani motsi da suke zargi.

Read also

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

A wani labarin kuma kunji cewa Yan bindiga sun kashe yan sanda, Lauyoyi tare da kona fasinjojin wata mota

Lamarin ya faru ne a ƙauyukan Isu and Onicha Igboeze, dake ƙaramar hukumar Onicha a cikin jihar Ebonyi.

Wannan na zuwa ne ƙasa da awanni 24 bayan gwamnan jihar Dave Umahi, ya yi barazanar kama iyayen yan bindiga.

Source: Legit.ng

Online view pixel