Wata jami'a ta sanya wa tsangaya sunan shahararriyar mawakiya Magajiya Danbatta

Wata jami'a ta sanya wa tsangaya sunan shahararriyar mawakiya Magajiya Danbatta

  • Jami'ar Maryam Abacha ta sanya wa wani yankin jami'ar sunan wata mawakiyar Hausa
  • A makon da ya gabata ne mawakiyar Hausa Halima Malam-Lasan wacce aka fi sani da Magajiya Danbatta
  • Jami'ar ta bayyana irin kokarin marigayiyar tare da cewa, an ba ta lambar yabo ne saboda gudunmawar da ta ba ilimi

Nijar - Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), ta sanya wa ginin sashen koyar da shari’a na jami’ar sunan mawakiyar Hausa, Halima Malam-Lasan, wacce aka fi sani da Magajiya Danbatta.

Daily Nigerian ta rahoto cewa Marigayi Danbatta ya rasu tana da shekaru 85 bayan gajeriyar rashin lafiya a Babban Asibitin Danbatta ranar Juma'ar da ta gabata.

Shugaba kuma wanda ya kafa MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo, daga Faransa ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya aikawa manema labarai a Kano ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

Jami'a ta sanya wa 'Faculty' sunan marigayi Magajiya Danbatta
Marigayiya Halima Malam-Lasan | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar sanarwar, mahukuntan jami’ar sun yanke wannan shawara ne ganin irin gagarumar gudunmawar da marigayi Danbatta ta bayar ga ilimi, musamman a Arewacin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Mista Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Franco-British International University a Kaduna, mahukuntan sun kuma ba da digirin girmamawa bayan mutuwa ga wakokin ta na Hausa.

Ya ce cibiyar ta yi niyyar ba ta lambar yabo lokacin tana raye amma ta mutu kafin taron girmamawar.

Mista Gwarzo ya bayyana cewa: "ban da sanya wa Kwalejin Shari'a sunan ta, za mu yi kewar kokarinta da shahararrun wakokinta."

Shugaban ya kuma bayyana rasuwar shahararriyar mawakiyar ta Hausa a matsayin babban rashi ga daukacin mutanen Arewacin Najeriya.

Shahararriyar mawakiyar Hausa, Magajiya Danbatta, ta rigamu gidan gaskiya

Shahararriyar mawakiyar Hausa, Magajiya Danbatta, ta rigamu gidan gaskiya tana da shekaru 86 a duniya.

Kara karanta wannan

Shahararriyar mawakiyar Hausa, Magajiya Danbatta, ta rigamu gidan gaskiya

A rahoton BBC Hausa, Magajiya ra rasu ne bayan fama da wata yar gajeruwar rashin lafiya a gidanta dake Danbatta, ranar Jumu'a da yamma.

Babban editan jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya jagoranci kaddamar da asusun tallafa wa mawakiyar a watan Disamba na shekarar 2019.

A wannan lokacin mawakiyar dake zaune a garin Danbatta, jihar Kano, ta samu kudi kimanin miliyan 5m, wanda aka yi amfani wajen gina mata gida da kuma sauran harkokin yau da kullum.

Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu

A wani labarin, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada N100,000 ga kowanne iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu a hatsarin motar da ya kashe mutum 16 yan Danbatta a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar ya fitar ta ce gwamnan ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasun a karamar hukumar Danbatta na jihar Kano.

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan

Anwar ya ce gwamnan ya bawa kowannensu N100,000 a cikin sanarwar da ya fitar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.