Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu

Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu

- Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya ziyarci iyalan mutum 16 'yan garin Danbatta da suka rasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Bayan yi musu ta'aziyya, Gwamna Ganduje ya bawa kowanne iyalan wadanda suka mutu kyautar naira 100,000

- Gwamnan ya tunatar da su cewa abinda ya faru kaddara ne daga Allah ya kuma shawarce su da su cigaba da yiwa mamatan addu'a

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada N100,000 ga kowanne iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu a hatsarin motar da ya kashe mutum 16 yan Danbatta a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar ya fitar ta ce gwamnan ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasun a karamar hukumar Danbatta na jihar Kano.

Hotuna: Ganduje ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu a hatsarin mota
Hotuna: Ganduje ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu a hatsarin mota. Hoto: @dawisu
Asali: Twitter

Hotuna: Ganduje ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu a hatsarin mota
Hotuna: Ganduje ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu a hatsarin mota. Hoto: @dawisu
Asali: Twitter

Anwar ya ce gwamnan ya bawa kowannensu N100,000 a cikin sanarwar da ya fitar, Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

A cewar sanarwar, iyalan wadanda suka rasun da suka fito daga wurare daban daban a karamar hukumar sun taru a wuri daya gabanin zuwan gwamnan.

"Mun samu sanarwar hatsarin da ya yi sanadin rasuwar mutum 16 daga karamar hukumar Danbatta da guda daya daga karamar hukumar Kura, abin bakin cikin ya girgiza mu," in ji Ganduje.

Ya tunatar da iyalan cewa su tuna duk abinda ya faru kaddara ce daga Allah ya kuma shawarce su da su cigaba da yi wa wadanda suka rasu addua'a.

KU KARANTA: Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi

Daya daga cikin 'yan uwan wadanda suka rasun da ya wakilci sauran, Sulaiman Muhammad, ya yabawa gwamnan bisa kyautar da ya yi musu da damuwa da ya nuna kan abinda ya faru.

"Munyi farin cikin ganin gwamna ya ziyarce mu," in ji shi.

Da farko dai rahotanni sun ce 'yan bindiga ne suka kashe mutanen 'yan asalin karamar hukumar Danbatta a hanyarsu ta zuwa Legas daga Kano.

Amma daga bisani rundunar 'yan sanda da wasu majiyoyin sun tabbatar da cewa hatsarin mota ce ta yi ajalinsu.

A wani labarin, Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Kasa, FRSC, reshen jihar Adamawa ta ce a ƙalla mutane 40 ne suka rasu sakamakon hatsarin mota daga watan Satumba zuwa 9 ga watan Disamba.

Hukumar ta kuma ce mutum 203 sun samu mabanbantan raunuka, Vanguard ta ruwaito.

Mista Ocheja Ameh, kwamandan FRSC na Adamawa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Juma'a a Yola cewa an kuma samu hatsarin mota 82 daga Satumba zuwa 9 ga watan Disamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel