Shahararriyar mawakiyar Hausa, Magajiya Danbatta, ta rigamu gidan gaskiya

Shahararriyar mawakiyar Hausa, Magajiya Danbatta, ta rigamu gidan gaskiya

  • Ɗaya daga cikin mawakan Hausa mata da suka shahara, Magajiya Ɗanbatta, ta rigamu gidan gaskiya
  • Rahoto ya nuna cewa Magajiya ta rasu tana da shekaru 86 a duniya a gidanta dake Ɗanbatta, jihar Kano
  • Mawakiyar ta shahara sosai a ɓangaren wakar Hausa tsakanin shekarar 1970 zuwa 1980 a Makoɗa dake jihar Kano

Kano - Shahararriyar mawakiyar Hausa, Magajiya Danbatta, ta rigamu gidan gaskiya tana da shekaru 86 a duniya.

A rahoton BBC Hausa, Magajiya ra rasu ne bayan fama da wata yar gajeruwar rashin lafiya a gidanta dake Ɗanbatta, ranar Jumu'a da yamma.

Marigayya Magajiya Danbatta
Shahararriyar mawakiyar Hausa, Magajiya Danbatta, ta rigamu gidan gaskiya Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Babban editan jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya jagoranci kaddamar da asusun tallafa wa mawaƙiyar a watan Disamba na shekarar 2019.

A wannan lokacin mawakiyar dake zaune a garin Danbatta, jihar Kano, ta samu kuɗi kimanin miliyan 5m, wanda aka yi amfani wajen gina mata gida da kuma sauran harkokin yau da kullum.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wace irin shahara ta yi a fagen waka?

Magajiya Ɗanbatta na ɗaya daga cikin mawakan Hausa da tauraruwarsu ta haska daga 1970 zuwa 1980, amma lokaci ɗaya aka mance da ita.

Kafin Jaafar Jaafar ya dawo da labarinta, Magajiya ta samu lalurar makanta, inda ta koma bara a garin Makoɗa, cikin jihar Kano.

Jaafar ya yi wani rubutu a watan Disamba, 2019, yace:

"Na gamu da Mawakiya Magajiya Ɗanbatta a gidanta dake Makoɗa, Kano. Lokacin da na buga wani hoton bidiyon waƙarta, wani abokina ya shaida mun cewa tana raye."

A wani labarin na daban kuma Wani mutumi, Kenneth Nwoha, ya sheƙe matarsa mai ƙaunarsa da ɗan da suka haifa, sannan ya jikkata mutanen Anguwa shida

Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin na zargin cewa mutumin ya samu taɓin kwakwalwa ne cikin kankanin lokaci.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah, yace an kaiɓmutumin asibiti domin duba cikakkar lafiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel