Ya kamata Buhari ya yage tsarin mulkin 1999, saboda kakaba mana shi aka yi, Bakare
- Wani fasto a jihar Legas ya bayyana bukatar a yage kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999
- Ya bayyana cewa, kundin tsarin ba komai bane face takardar shaidar mutuwa ga 'yan kasar
- Ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su tashi tsaye domin dawo da martabar kasar a idon duniya
Legas - Mai kula da cocin CGCG da ke jihar Legas, Fasto Tunde Bakare, ya roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya jagoranci canjin kundin tsarin mulkin 1999, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce kundin tsarin mulkin na yanzu shi ne jigon matsalar da ke fuskantar Najeriya, yana mai bayyana shi a matsayin “daukakiyyar takardar shaidar mutuwa.”
Da yake magana a gidan rediyo a jihar Legas, Bakare ya kalubalanci Buhari da ya daina mika wa Majalisar Dokoki ta kasa komai.
Ya roki Buhari da ya “rusa wannan kundin tsarin mulkin da ba shi da inganci.”
Ya ce tsarin mulkin 1999 wanda aka fara da, "Mu Jama'a" sojoji ne suka kakabawa 'yan Najeriya shi.
Bakare ya sake nanata cewa sake fasalin Najeriya da sauya kundin tsarin mulki ya fi muhimmanci fiye da tattauna batun canjin mulki.
Ya kuma ba da sanarwar kafa gangamin Najeriya don 'Yan Najeriya (N4N) domin dawo da martabar Najeriya.
A cewarsa, an kaddamar da gangamin na N4N ne saboda lokaci ya yi da 'yan Najeriya za su dawo da martabar kasarsu.
A cewarsa:
"Za a sami canjin gwamnati a 2023."
Babu tsarin karba-karba na shugabancin kasa a kundin tsarin mulkin APC, Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ta ce tsarin shugabancin kasa na mulkin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin jam’iyya mai mulki ta APC.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin taron nada shugaban wata kungiyar matasan arewa a Kaduna inda ya ce matasan Najeriya ne suke da alhakin zaben shugaban kasa.
Daily Trust ta ruwaito yadda rantsarwar kungiyar da suke kira YBN ta kasance wanda bai kai kwana 3 ba da kungiyar dattawan arewa ta NEF ta ce akwai yuwuwar arewa ta ci nasarar zaben 2023 saboda ta na da yawan da za ta iya cin zaben shugaban kasa.
Bello wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman na harkokin matasa da dalibai, Ahmed Jubril, ya ce cigaba mai kyau ne matasan Najeriya su dinga tallafa wa 'yan uwan su wurin neman mukami babba kamar shugaban kasan Najeriya.
Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista
A wani labarin, Ministan Ayyuka da Gidaje na Najeriya, Babatunde Fashola, ya ce dole ne 'yan Najeriya su san ilimi da horon da shugaban kasa Muhammadu ya samu don fahimtar tasirin sa kan mulki.
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin shiri mai taken, 'The Effect Buhari: Undeniable Achievements', wanda aka watsa a gidan Talabijin na Channels a yammacin Asabar 9 ga watan Oktoba.
Shirin na awa daya ya ba da labarin wasu “nasarori” na gwamnatin Buhari a duk fannonin shugabanci da suka hada da ci gaban ababen more rayuwa, gidaje, noma, sufuri, kiwon lafiya, da sauran su.
Asali: Legit.ng