Na matsu sosai, zan biya sadaki kuma zan ɗau nauyin komai, Wata kyakkyawar budurwa na neman mijin Aure

Na matsu sosai, zan biya sadaki kuma zan ɗau nauyin komai, Wata kyakkyawar budurwa na neman mijin Aure

  • Wata budurwa ta cire kunya ta fito kan titi tana neman mijin da zai aure ta tsakani da Allah
  • Matar tace tana da kuɗi kuma ta yi alkawarin ɗaukar nauyin aurenta, bata son mijinta ya wahala
  • Ta kara da cewa ba wannan ne karon farko da ta fito neman miji ba, kuma zata cigaba da ɗaukar matakin da ya dace kafin lokaci ya ƙure mata

Tanzania- Wata kyakkyawar budurwa ta cire kunya ta fito neman mijin aure kan titi ɗauke da allon rubutu a yankin Buza da ke birnin Daris Salaam na kasar Tanzaniya, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Hakanan kuma budurwar ta bayyana cewa yawan shekarun namiji bai dame ta ba, bukatarta shine cika burinta na yin aure.

Read also

Yadda mata ke amfani da Hijabi wajen safarar muggan makamai ga yan fashi a Najeriya

A wani hoton bidiyo da ya watsu, budurwar ta fito kan titi ɗauke da allo, wanda ke ɗauke da rubutun, "Ina neman mijin aure da ke tsakanin shekara 20 zuwa 70.”

Mata na neman miji a Tanzaniya
Na matsu sosai, zan biya sadaki kuma zan ɗau nauyin komai, Wata kyakkyawar budurwa na neman mijin Aure Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Ni budurwace har yanzun

Budurwar ta bayyana cewa ta ɗauki nauyin al'amuran bikin auren ta, kama daga sadaki da sauransu, kuma a cewarta har yanzun ita budurwace, ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba.

Tace:

"Na ɗauki nauyin biyan sadaki, kuma tuni na tanaji zoben aure na, zan siya wa angon kayan da zai saka ranar biki, fatana in samu miji mai tsoron Allah."

Ko meyasa ta fito kan titi neman miji?

A cewarta, tana tsoron lokaci ya ƙure ba ta yi aure ba, don haka ya zama tilas a kanta ta ɗauki matakin da ya dace don kaucewa matsala.

Read also

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

"Kullum kara yawan shekaru nake ina ƙara tsufa, kuma ina bukatar namiji a tare da ni. Ina da yaƙinin cewa ban karya doka ba, ni na yanke wa kaina shawarar daukar wannan matakin."

Ina da kuɗi kuma zan ɗauki nauyin komai

Matar ta ƙara jaddada cewa ita mai kuɗi ce, a don haka babu wata matsala da ta shafi kuɗi matukar ta samu mijin da zai neme ta da aure.

A cewarta, ba wannan ne farkon da ta fito neman mijin aure ba, ta yi a baya, kuma zata cigaba da yin haka har sai ta cimma burinta.

A wani labarin kuma mun kawo muku Yadda mata ke amfani da Hijabi wajen safarar muggan makamai ga yan fashi a Najeriya

Wasu mata biyu da jami'an yan sanda suka cafke sun bayyana yadda suke tallafawa yan fashi ta hanyar amfani da Hijabi.

Matan sun bayyana yadda suke ɗaukar bindigu AK-47 daga wani wuri a umarce su kai ta wani wuri.

Read also

Yan sakai sun hallaka limamin masallaci da wasu mutum 10 a jihar Sokoto

Source: Legit

Online view pixel