Kotun Isra'ila ta haramtawa Yahudawa zuwa kusa da masallacin Kusu da sunan ibada

Kotun Isra'ila ta haramtawa Yahudawa zuwa kusa da masallacin Kusu da sunan ibada

  • Kotu a Isra'ila ta haramtawa Yahudawa yin ibada a harabar masallacin Kudus da musulmi ke ibada
  • A baya wata kotu ta yanke hukuncin dakatarwa kan wani malamin Yahudawa da ya yi ibada a wajen
  • An sha samun rikice-rikice tsakanin Muslmai da Yahudawa a yankin saboda sabanin ra'ayoyi

Isra'ila - Kotun Isra’ila ta amince da haramcin ibadar Yahudawa a harabar Masallacin Kudus, tare da yin watsi da hukuncin karamar kotu da ya haifar da rikici tsakanin Falasdinawa da duniyar Musulmi.

An yi wa Aryeh Lippo, malamin Yahudawa, hukuncin haramcin makwanni biyu daga harabar masallacin a watan da ya gabata bayan yin ibada a can, Aljazeera ta ruwaito.

Sai dai, a ranar Talata kotun Kudus ta soke hukuncin, tana mai cewa ibadar da Lippo ya yi “bai saba wa umarnin 'yan sanda ba”.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekaru 70 da wasu 2 dauke da makamai

Kotun Isra'ila ta haramtawa Yahudawa zuwa kusa da masallacin Kusu da sunan ibada
Ibada a bakin masallacin Kudus | Hoto: france24.com
Asali: UGC

An ba wa Yahudawa damar ziyartar rukunin ginin masallacin amma ba za su yi addu'a ko ayyukan ibada a can ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Falasdinawa sun yi tir da hukuncin da kotun Isra’ila ta yanke, wanda ya inganta yarjejeniya mai tsawo wacce Musulmai ke yin ibada a Kudus - wuri na uku mafi tsarki na Musulunci - yayin da Yahudawa ke yin ibada a bangon Yammaci da ke kusa.

'Yan sandan Isra'ila sun daukaka kara kan hukuncin karamar kotun a ranar Talata, kuma Alkalin Kotun Kudus Aryeh Romanoff a ranar Juma'a ya amince da haramcin.

Falasdinawa, da jami'ai a Jordan, Masar da Saudi Arabiya sun yi Allah wadai da hukuncin kotun.

Wurin mai alfarma ga Musulmai a matsayin wuri mai tsarki, Yahudawa na girmama shi a matsayin tsohon wurin ibada, masallacin da filin da ke kewaye da shi sun dade suna fuskantar a rikicin Isra’ila da Falasdinawa.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

Jaridar France24 ta ruwaito cewa, Isra’ila ta kame Kudus ta Gabas ciki har da masallacin a 1967, amma Jordan ita ce mai kula da wuraren Musuluncin a birnin.

Babu wata dokar Isra’ila da ta hana Yahudawa ibada a harabar Masallacin Kudus, amma tun 1967, hukumomin Isra’ila sun aiwatar da dokar hana tashe-tashen hankali.

A cikin wata sanarwa da ke goyon bayan haramcin 'yan sanda a ranar Juma'a, Ministan Tsaron Jama'a na Isra'ila Omer Bar-Lev ya yi gargadin cewa sauyin yanayin da ake ciki zai "kawo barazana ga zaman lafiyar jama'a".

Kasar Isra'ila ta tsorata bayan mai tsattauran ra'ayi a kasar Iran ya lashe zabe

Rahoton da Legit.ng Hausa ta nakalto daga BBC ya bayyana cewa, Isra’ila ta shiga damuwa kan zaben Ebrahim Raisi a matsayin sabon shugaban kasar Iran.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Isra’ila, Lior Haiat, ya ce Mista Raisi shi ne shugaban kasar Iran mafi tsaurin ra’ayi da aka taba yi a tarihi.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Babu abun da Arewa za ta rasa, in ji jigon APC

Ya yi gargadin cewa shugaban zai ci gaba da inganta ayyukan nukiliyar kasar Iran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel