2023: Har yanzu ina tuntubar Allah akan ko na tsaya takarar sanata, inji Ortom

2023: Har yanzu ina tuntubar Allah akan ko na tsaya takarar sanata, inji Ortom

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi martani akan batun cewa ko zai tsaya takarar sanata bayan kammala wa'adinsa na biyu a matsayin gwamna
  • Ortom ya ce a halin yanzu dai bai yanke hukunci ba domin yana tuntubar Allah ne tukuna a kan lamarin
  • Ya ce a matsayinsa na wanda ke aiki da hukuncin Allah a kansa a koda yaushe, zai yi takara idan Ya bashi iko, sannan zai hakura idan Allah ya nemi yayi hakan

Benue - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce har yanzu bai yanke shawara kan ko zai tsaya takarar kujerar sanata a zaben 2023 ba.

Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, Ortom ya fadi hakan ne a ranar Asabar, 9 ga watan Oktoba yayin da yake zantawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

2023: Har yanzu ina tuntubar Allah akan ko na tsaya takarar sanata, inji Ortom
2023: Har yanzu ina tuntubar Allah akan ko na tsaya takarar sanata, inji Ortom Hoto: Vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake amsa tambaya kan ko zai yi takara bayan ya kammala wa’adinsa na gwamna, Ortom ya ce zai dauki matakin ne daidai da abin da Allah ya yarda.

“Har yanzu ina tuntubar Allah domin ba na yanke shawara ba tare da na tuntubi Allahna ba. Idan ya ce eh, zan ci gaba da yin takara, amma idan Ya ce a'a, zan yi biyayya da shawarar da ya yanke, ” inji shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya kuma ce ya kamata a yi watsi da rahotannin rarrabuwar kawuna a cikin Jam’iyyar PDP, saboda mambobi suna aiki cikin hadin kai, Vanguard ta kuma ruwaito.

Ya ce:

“PDP a matsayin jam’iyya ta yi kurakurai a baya kuma ta koyi darussa da yawa daga kurakuranta kuma ta shirya tsaf don karbe shugabancin kasar daga hannun APC.

Kara karanta wannan

Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna

“Kada wanda ya yaudare ku cewa PDP ta rarrabu. Muna aiki tare a matsayin jam’iyya.
“Mun hadu kuma mun amince cewa mukaman da suke arewa a yanzu su koma kudu, yayin da na kudu za su koma arewa.
“Wannan shine ƙudirin kwamitin shiyya kuma an yarda da shi a matakin ƙasa.
"Babu wanda ya yi watsi da hukuncin. Duk yan PDP sun yarda da shi.”

Gwamnonin Jam'iyyar PDP Sun Cimma Matsaya Kan Yankin da Zai Fitar da Shugaba

A wani labarin, gwamnonin da suka ɗare mulki ƙarƙashin jam'iyyar PDP sun amince a kai shugaban jam'iyya na gaba yankin arewa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wannan mataki da gwamnonin suka ɗauka wata babbar alama ce dake nuna cewa tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023 zai tafi yankin kudu.

Rahoto ya nuna cewa a wurin taron gwamnonin PDP, ranar Laraba, wanda ya gudana a gidan gwamnan Akwa Ibon na Abuja, sun kaɗa kuri'a 9-3 kan arewa.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng