Gwamnonin Jam'iyyar PDP Sun Cimma Matsaya Kan Yankin da Zai Fitar da Shugaba

Gwamnonin Jam'iyyar PDP Sun Cimma Matsaya Kan Yankin da Zai Fitar da Shugaba

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun kaɗa kuri'ar amincewa shugaban jam'iyya na gaba ya fito daga yankin arewacin Najeriya
  • Rahotanni sun bayyana cewa wannan wata babbar alama ce dake nuna babbar jam'iyyar hamayya zata kai tikitin shugaban ƙasa yankin kudu
  • Daga cikin gwammonin PDP na arewa, akwai waɗanda suke da muradin neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 karkashin PDP

Abuja - Gwamnonin da suka ɗare mulki ƙarƙashin jam'iyyar PDP sun amince a kai shugaban jam'iyya na gaba yankin arewa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wannan mataki da gwamnonin suka ɗauka wata babbar alama ce dake nuna cewa tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023 zai tafi yankin kudu.

Rahoto ya nuna cewa a wurin taron gwamnonin PDP, ranar Laraba, wanda ya gudana a gidan gwamnan Akwa Ibon na Abuja, sun kaɗa kuri'a 9-3 kan arewa.

Kara karanta wannan

Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya

Gwamnonin Jam'iyyar PDP
Gwamnonin Jam'iyyar PDP Sun Cimma Matsaya Kan Yankin da Zai Fitar da Shugaba Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya zaɓen ya gudana?

Gwamnonin arewa guda uku, Bala Mohammed (Bauchi), Adamu Fintiri (Adamawa) and Darius Ishaku (Taraba), sune suka zaɓi a kai kujerar shugaban jam'iyya yankin kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ya bayyana kudirinsa na neman tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa karkashin PDP a zaɓen 2023.

Gwamna ɗaya tilo da ya fito daga jihar Arewa kuma ya kaɗa kuri'ar kawo shugaban PDP arewa, shine gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, bai kaɗa kuri'arsa ba, saboda shi ya jagoranci taron.

Bugu da ƙari, shima ana hasashen yana harin tikitin takarar shugaban ƙasa, duk da rashin nasarar da ya yi a zaɓen fitar da gwani na 2019.

Gwamnonin da suka amince shugaba ya fito daga Arewa

Gwamnonin da suka kaɗa kuri'ar shugaban PDP ya fito daga yankin arewa sun haɗa da, Seyi Makinde (Oyo), Godwin Obaseki (Edo), Nyesom Wike (Rivers), da Udom Emmanuel (Akwa Ibom).

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

Sauran sune, Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Okowa (Delta), da kuma Douye Diri (Bayelsa).

Idan har aka zaɓi ɗan arewa a matsayin shugaban jam'iyyar PDP, to alamu sun fara bayyana cewa PDP zata tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu.

A wani labarin kuma Attahiru Bafarawa yace Mutane sun shiga bala'i a yankin Arewa fiye da tunani musamman a Zamfara

Bafarawa yace matsalar tsaro ta kai yadda manoma sun kasa zuwa gonakinsu girbin abinda suka noma saboda tsoron yan bindiga.

Ya yi kira ga gwamnan Zamfara da kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, su rinka ziyara zuwa jihohin wannan yanki don ganewa idonsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262