Ganduje ya sake kai wa Rimingado 'farmaki', 'yan sanda na shirya sabbin tuhuma

Ganduje ya sake kai wa Rimingado 'farmaki', 'yan sanda na shirya sabbin tuhuma

  • Rahotanni sun bayyana yadda Gwamna Ganduje na jihar Kano ke son a cigaba da tuhumar Barista Muhuyi Rimingado
  • Majiyoyi daga gidan gwamnati sun tabbatar da cewa Gwamna ya zargi Muhuyi da hannu kan tuhumar da EFCC ke wa Goggo
  • Duk da a baya 'yan sanda sun wanke Muhuyi, yanzu haka an sake mika sabbin tuhuma gaban wata kotun majistare a Noman's Land

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar na cigaba da kokarin mika sabbin tuhuma ga dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado, kan zarginsa da ake da mika bayanan bogi gaban majalisar jihar Kano.

Idan za mu tuna, majalisar Kano ta gayyaci Rimingado domin ya bayyana a gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar bayan korafin da aka mika gaban ta a ranar 14 ga watan Yuli.

Read also

Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista

Amma yayin dogaro da halin rashin lafiya tare da hadawa da takarda, Rimingado ya bukaci asalin kwafin korafin da aka mika gaban majalisar tare da bukatar karin lokaci kafin ya bayyana.

Ganduje ya sake kai wa Rimingado 'farmaki', 'yan sanda na shirya sabbin tuhuma
Ganduje ya sake kai wa Rimingado 'farmaki', 'yan sanda na shirya sabbin tuhuma. Hoto daga dailynigerian.com
Source: UGC

A ranar 19 ga watan Yuli, asibitin kasa ya rubuto wa majalisar jihar Kano wasika cewa wannan takardun asibiti da aka mika gaban ta na bogi ne.

A wasikar mai kwanan wata 19 ga Yuli tare da lamba NHA/CMAC/GC/0117/2021/V.I/01 wacce Dr. A. A. Umar ya saka hannu, ya ce takardar da aka samu ta jabu ce.

A sakamakon wannan martanin, 'yan sandan jihar Kano sun gayyaci Rimingado domin ya amsa tambayoyi kan takardun jabu.

Amma bayan bincike, majiyoyin Daily Nigerian sun tabbatar mata da cewa ba a kama shi da laifi ba kuma an mayar masa da fasfotinsa.

Read also

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

Sabon Rikici

A bayyane ya ke gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje bai gamsu da yadda 'yan sanda suka rike lamarin ba, hakan yasa ya jaddada cewa a sake nemo wasu tuhume-tuhumen.

Majiyoyi a gidan gwamnati sun ce gwamnan ya sakankance cewa kama matarsa da EFCC ta yi duk Rimingado ne ya assasa.

"Gwamnan ya fusata da Muhuyi kan gayyatar da EFCC ta yi wa matarsa. Kowa ya yarda cewa Muhuyi ne yayi sanadin hakan," majiyar da ta bukaci a rufe sunanta ta sanar.

Gwamnan ya fusata da binciken da EFCC su ke wa matarsa kan wani tallafin ilimi na bankin duniya mai suna BESDA wanda hukumar yaki da rashawan ta gayyaci shugaban SUBEB, Danlami Hayyo domin tuhumarsa.

Sama da biliyan biyu ne aka yi sama da fadi da shi ta wani kamfani mai suna Global Firm Ltd, wanda ya ke da alaka da iyalan.

Majiyar cikin gida ta sanar da Daily Nigerian cewa tuni 'yan sanda sun mika rahoton farko gaban wata kotun majistare da ke Noman's Landa wacce ke samun shugabancin Aminu Gabari.

Read also

Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

Hakan ya na nufin a kowanne lokaci Muhuyi zai iya jin sammaci.

Kano: Dalibar jami'ar Bayero ta tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

A wani labari na daban, dalibar jami'ar Bayero da ke Kano wacce masu garkuwa da mutane suka sace a tsakar birnin Kano mai suna Sakina Bello, ta tsero daga hannun miyagun da suka sace ta.

Idan za a tuna, dalibar aji ukun da ke karantar fannin ilimin tsirrai, an sace ta wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata yayin da ta ke hanyar zuwa gida a Keke, LIB ta ruwaito.

Daga bisani, wadanda suka yi garkuwa da ita sun kira 'yan uwan ta da safiyar Laraba tare da bukatar kudin fansa har miliyan dari, LIB ta wallafa.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel