Kasafin Kudi: Za'a kashe N35m wajen kwashe Masai a Aso Villa, a 2022
- Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2022 gaban majalisar dokokin tarayya
- Shugaban kasan ya yiwa Kasafin Kudin taken 'Kasafin kudin cigaba da girman tattalin arziki
- Buhari ya bayyana cewa Ministar Kudi za tayi bayanin kasafin kudin ga yan Najeriya
- Za a kashe kimanin milyan takwas wajen yaki da rashawa a Aso Villa
Abuja - Duk da kudaden da aka kebancewa hukumar EFCC da ICPC, fadar shugaban kasan ta shirya kashe N7.34 million wajen yaki da rashawa a 2022.
Wannan na kunshe cikin daftarin kasafin kudin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis, 7 ga Oktoba, 2021.
A lamba ta 22021017, za'a bukaci N7,341,583 donyaki da rashawa a fadar shugaban kasa kadai/
Hakazalika, shugaba Buhari ya bukaci N35.41 million don yashe shaddar fadar shugaban kasa.
Kudin kwashe masai mai lamba 22020206 ya kasance abinda ake bukata koda yaushe don kwashe masai a fadar shugaban kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bugu da kari, an kebance N55.05million don gyare-gyaren gidajen da ke fadar shugaban kasa.
Kuma an ware N5.17bn don gyare-gyaren ofishohi.
Buhari da Osinbajo zasu kashe N3.2bn wajen tafiya-tafiye a 2022
Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, zasu kashe N3.2 billion wajen tafiye-tafiye kadai a shekarar 2022 da muke dunfara.
A bayanan kudaden, shugaban kasan zai kashe N2.3billion wajen tafiye-tafiye da sufuri na ofishinsa yayinda shi kuma mataimakinsa aka shirya masa N778.2 million.
Hakazalika fadar shugaban kasar aka kebe mata N162.25 million don sufuri.
A shekarun baya, rahotanni sun nuna cewa shugaba Buhari da mataimakinsa sun kashe N1.5 billion a 2019 don tafiye-tafiye da abinci; N1.52 billion a 2018; N1.45 billion a 2017 ; sannan N1.43 billion da 2016.
Asali: Legit.ng