Kasafin kudin 2022: Buhari ya bukaci N644.3m matsayin kudin abinci, N76.6m na kudin haya
- An saki daftarin kasafin kudin 2022 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisar dokoki
- A jerin kudaden, fadar shugaban kasa na son kashe N76.6m wajen biyan kudin haya
- Hakazalika an ware kudade na musamman don kayan abinci da shakatawa
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da jerin kudaden da yake bukatan kashewa a hedkwatar mulki, Fadar Aso Villa, a shekarar 2022 da zamu shiga nan yan watanni uku.
Kasafin kudin fadar Aso Villa ya hada da N12.31 billion na hedkwata gaba daya, yayinda aka bukaci N24.83 billion don ayyukan sashen shugaban kasa.
Hakazalika, ofishin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, zai kashe N1.18 billion.
Wannan na kunshe cikin daftarin kasafin kudin da Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis, 8 ga Okotoba, 2021.
Bayani dalla-dalla kan kudaden ya nuna cewa an ware N644.3 million don abinci da kayan shakatawa, sannan za'a kashe N76.6 million don biyan kudin haya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kasafin kudin bara, an biya kudin hayan N66.6 million kuma wannan ya zama wani abu ake biya kowace shekara.
Dalla-dallan kudin abinci da alatun girki
Kudin danyen kayan abinci da alatun girki hedkwata- N135.66 million
Kudin danyen kayan abinci da alatun girki na gidan shugaban kasa - N301.13 million
Kudin danyen kayan abinci da alatun girki na gidan mataimakin shugaban kasa - N156.66 million
Asali: Legit.ng