Kasafin kudin 2022: Buhari da Osinbajo zasu kashe N3.2bn wajen tafiya-tafiye a 2022

Kasafin kudin 2022: Buhari da Osinbajo zasu kashe N3.2bn wajen tafiya-tafiye a 2022

  • Tun bayan hawan mulki, Shugaba Buhari yayi tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya daban-daban
  • Yayinda wasu tafiye-tafiye na aiki ne, wasu kuwa na zuwa jinyan kansa ne
  • A lissafin da akayi, Shugaba Muhammadu Buhari ya fita daga Najeriya akalla sau 51 daga 2015 kawo yanzu

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, zasu kashe N3.2 billion wajen tafiye-tafiye kadai a shekarar 2022 da muke dunfara.

Wannan na kunshe cikin kasafin kudin 2022 da Buhari ya gabatar gaban yan majalisa ranar 8 ga Okotba 2021 domin su duba kuma su amince da shi.

A bayanan kudaden, shugaban kasan zai kashe N2.3billion wajen tafiye-tafiye da sufuri na ofishinsa yayinda shi kuma mataimakinsa aka shirya masa N778.2 million.

Hakazalika fadar shugaban kasar aka kebe mata N162.25 million don sufuri.

Kara karanta wannan

Kasafin Kudi: Za'a kashe N35m wajen kwashe Masai a Aso Villa, a 2022

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasafin kudin 2022: Buhari da Osinbajo zasu kashe N3.2bn wajen tafiya-tafiye a 2022
Kasafin kudin 2022: Buhari da Osinbajo zasu kashe N3.2bn wajen tafiya-tafiye a 2022 Hoto: Preseidency
Asali: Facebook

Bayani dalla-dalla

Ofishin Buhari

1. Tafiye-tafiyen cikin Najeriya - N775.6 million

2. Tafiye-tafiye zuwa kasar waje - N1.53 billion

Ofishin Osinbajo

1. Tafiye-tafiyen cikin Najeriya - N301.9 million

2. Tafiye-tafiye zuwa kasar waje - N476.2 million

A shekarun baya, rahotanni sun nuna cewa shugaba Buhari da mataimakinsa sun kashe N1.5 billion a 2019 don tafiye-tafiye da abinci; N1.52 billion a 2018; N1.45 billion a 2017 ; sannan N1.43 billion da 2016.

Asali: Legit.ng

Online view pixel