2023: Ina gabatar da Atiku ga 'yan Najeriya, babu dan takarar kudu da zai iya lashe zabe – Jigon PDP

2023: Ina gabatar da Atiku ga 'yan Najeriya, babu dan takarar kudu da zai iya lashe zabe – Jigon PDP

  • Fitaccen jigon jam'iyyar PDP, Raymond Dokpesi, ya bayyana goyon bayansa ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku don zama shugaban Najeriya a 2023
  • Dokpesi ya ce babu wani a duk fadin yankin kudancin kasar da zai iya lashe kujerar shugabancin jam'iyyar adawar a 2023
  • Sai dai kuma, babban jigon na PDP, ya ce duk wanda ya zama shugaban Najeriya to ya lallashi yankin kudu maso gabas

Cif Raymond Dokpesi, jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya ce babu dan takarar kudu da zai iya lashe wa jam’iyyarsa zaben shugaban kasa na 2023.

Dokpesi ya yi wannan ikirarin ne a cikin wata hira da jaridar Daily Trust ta buga a ranar Asabar, 9 ga Oktoba.

2023: Ina gabatar da Atiku ga 'yan Najeriya, babu dan takarar kudu da zai iya lashe zabe – Jigon PDP
2023: Ina gabatar da Atiku ga 'yan Najeriya, babu dan takarar kudu da zai iya lashe zabe – Jigon PDP Hoto: Atiku Abubakar, Dr Kemi Omololu-Olunloyo
Asali: Facebook

Da aka tambaye shi ko ba ya goyon bayan kiran da ake yi na PDP ta gabatar da dan takara daga kudu maso gabas a 2023, jigon na PDP ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnonin kudu maso gabas sun yanke hukunci na ƙarshe kan shugabancin 2023

"Babu wani dan takara daga kudu maso gabas, na maimaita cewa babu wani dan takara daga kudu da za ku saka a arewa a yau wanda zai iya cin nasara. Zai zama babban kalubale."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai bukatar a biya yankin kudu maso gabas diyya

Koda yake yace babu wani dan takara daga kudu maso gabas da zai iya yin nasara a 2023, Dokpesi ya ce yankin ya cancanci samun kujerar idan aka mika kujerar shugabanci zuwa yankin kudu.

Jigon na PDP ya kara da cewa duk wanda ya zama shugaban Najeriya dole ne ya yi dannar kirji ga mutanen kudu maso gabas.

Amma, ya ce ya kamata PDP ta nemi dan takararta na 2023 daga yankin arewa.

Atiku Abubakar shine dan takarar da zai kai labari a 2023 - Dokpesi

Kara karanta wannan

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

A halin da ake ciki, Dokpesi ya ce ya yi wa 'yan Najeriya tayin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, inda ya kara da cewa yana da duk abin da ake bukata don zama shugaban Najeriya a 2023.

Ya ce:

"Na tsaya tsayin daka don bayyana cewa Atiku Abubakar shine dan takarar da zai kai labari a 2023. Yana da cancanta, dan arewa ne mai sassaucin ra'ayi, wanda a shirye yake ya sadaukar da kansa."

Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace shugaban ƙasa na gaba zai iya fitowa daga kowane yanki, kamar yadda The cable ta ruwaito.

Atiku ya yi wannan magana ne ranar Alhamis a taron majalisar zartarwa (NEC) na babbar jam'iyyar hamayya PDP, wanda ya gudana a Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shine hanyar warware matsalolin da Najeriya ke fama da su ba.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel