2023: Abin da ya sa ba za a iya amincewa da Inyamuri a zaben Shugaban kasa ba inji Jigon APC
- Joe Igbokwe yace zai yi wahala mutane su yarda Ibo su zama Shugaban kasa
- Jigon na APC yana ganin sai dai mutanensa sun ajiye fafutukar Biyafara a gefe
- Duk da hakan, Igbokwe ya yarda cewa ba a yi wa yankin Ibo adalci a Najeriya
Lagos - Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Legas, Joe Igbokwe yace ba za a yarda da ‘dan takarar shugaban kasa daga yankin Ibo a zabe mai zuwa na 2023 ba.
Punch ta rahoto Joe Igbokwe yana cewa mutanen kasar nan ba za su kada kuri’a ga Ibo, wanda zai yi amfani da kujerar shugaban kasar wajen raba Najeriya ba.
Igbokwe wanda yana cikin masu ba Mai girma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, shawara ya bayyana wannan da ‘yan jarida suka yi hira da shi.
Ba ayi wa Ibo adalci a Najeriya?
Kamar yadda Igbokwe wanda shi kan shi Ibo ne ya bayyana, ba a yi wa mutanensa adalci a kasar.
“An yi wa yankin Kudu maso gabashin Najeriya rashin adalci sosai, duk abin da ake raba wa a kasar nan, mu ne muke samun kaso maras tsoka.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da rashin adalcin da yace ana yi wa mutanen bangaren Kudu maso gabas, Igbokwe yace tada rigima da kashe-kashen da ake yi ba za su taba zama mafita ba.
Igbokwe wanda ya taba rike kakakin APC a Legas, ya yi kaca-kaca da ‘yan IPOB da sauran masu tada kafar baya, yace sun dauki gwagwarmayarsu ta bai-bai.
A cewar Igbokwe, ‘yan kungiyar IPOB magoya-bayan jam’iyyar PDP ne wanda suka fara tada rikici tun da APC ta karbi mulkin Najeriya bayan zaben 2015.
“Idan ka na so sauran ‘yan Najeriya su zabe ku, sai ka hada-kai da jama’a, a kulla abokantaka.”
Ina mafita?
‘Dan siyasar ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara yawan jihohin Kudu maso gabas ta yadda yankin zai zama daidai da sauran bangarorin kasar.
Yankin na da jihohi biyar: Anambra, Imo, Enugu, Abia da Ebonyi, akasin shida da saura suke da su.
Zaben gwamnan Anambra
Dazu muka ji jam'iyyar PDP mai hamayya ta bakin Kola Ologbondiyan, ta ja-kunnen Gwamnatin cewa Tarayya ta ajiye maganar kakaba dokar ta-baci a jihar Anambra.
Nan da kwana 30 ake sa ran za a gudanar da zaben sabon Gwamna a Anambra. Ganin ana tsakar rikici a jihar ya sa gwamnati ta fara tunanin daukar wannan matakin.
Asali: Legit.ng