Jerin jihohi Najeriya 6 da zasu amfana da sabon tallafin COVID19 daga asusun NSSF

Jerin jihohi Najeriya 6 da zasu amfana da sabon tallafin COVID19 daga asusun NSSF

  • Asusun tallafi na NSSF ya baiwa hukumar lafiya a matakin farko NPHCDA gudummuwar miliyan N300m
  • A cewar NSSF, tallafin zai taimaka matuka wajen yiwa yan Najeriya rigakafin COVID19 a wasu jihohin Najeriya shida
  • Shugaban hukumar NPHCDA, Dakta Faisal Shu'aib, yace wannan haɗin kan da aka samu daga NSSF zai sa a samu ƙaruwar masu bukatar yin rigakafi

Abuja - Asusun bada tallafi na NSSF ya bada tallafin zunzurutun kuɗi miliyan N300m a wani ɓangaren gudunmuwarsa ga shirin allurar rigakafin COVID19 ga hukumar lafiya a matakin farko (NPHCDA).

A rahoton Dailytrust, asusun NSSF, ya bada wannan tallafi ne domin samun daidaito wajen rigakafin ga yan Najeriya masu matsakaicin karfi.

Asusun NSSF
Jerin jihohi Najeriya 6 da suka amfana da miliyoyin tallafin COVID19 daga asusun NSSF Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bugu da ƙari, ana tsammanin tallafin zai matukar taimakawa shirin allurar rigakafin COVID19 a jihohi guda shida dake faɗin yankunan Najeriya shida.

Kara karanta wannan

Bincike: Jerin gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yin kokari

Wane jihohi ne zasu amfana da tallafin?

Jihohin da zasu amfana da tallafin sun haɗa da Adamawa, Katsina, Ogun, Edo, Imo da kuma jihar Nasarawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bisa hasashen yiwa mutum 60 allurar rigakafin kullum a kowace tawaga daga 1 ga watan Oktoba, NSSF ta bayyana cewa za'a samu nasarar yin miliyan ɗaya zuwa 31 ga watan Disamba.

Shin wannan haɗin guiwa zai haifar da ɗa mai ido?

Da yake jawabi game da wannan haɗin guiwar, shugaban Asusun NSSF, Babatunde Folawiyo, yace:

"Haɗa ƙarfi da karfe tsakanin hukumar NPHCDA da NSSF zai samar da cikakken wayar da kai a kan amfanin yin rigakafin."

A nasa ɓangaren, Shugaban hukumar NPHCDA, Dakta Faisal Shu'aib, yace wannan haɗin guiwar zai taimaka wajen samun ƙaruwar masu yin allurar a Najeriya.

A wani labarin kuma dandalin sada zumunta na tuwita ya bayyana gamsuwarsa da bayanan shugaba Buhari na ranar samun yanci

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji sun sako shahararren jarumin Nollywood da suka damke

A cikin jawabinsa na ranar yancin kai, Buhari yace gwamnati a shirye take ta ɗage hanin amfani da twitter da zaran an cimma matsaya.

Kamfanin, wanda a halin yanzun baya aiki a Najeriya, yana fatan tattaunawa da FG yasa a bar shi ya cigaba da ayyukansa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel