Kano: Hotunan wani gidan azabtarwa da aka gano, an ceto maza da yara 47 da aka ɗaure da mari

Kano: Hotunan wani gidan azabtarwa da aka gano, an ceto maza da yara 47 da aka ɗaure da mari

  • Yan sanda a jihar Kano sun gano wani gidan azabatarwa duk da gwamnatin jihar ta haramta
  • An kama masu kula da gidan su biyu an kuma garzaya da wadanda aka ceto zuwa asibiti
  • 'Yan sandan sun ce za su gurfanar da masu gidan a gaban kotu da zarar an gama bincike

Jihar Kano - 'Yan sanda a jihar Kano a ranar Alhamis sun ceto kimanin mutane 47 da aka daure da mari a wani gidan azabtarwa da ke birnin na Kano kamar yadda BBC Pidgin ta ruwaito

An tarar da mutanen da rauni da dama a jikinsu kafin aka kwance su sannan aka garzaya da su asibitin Murtala Mohammed da ke Kano domin basu kulawa.

Read also

Yadda waɗanda aka yi garkuwa da su suka shafe kwanaki 53 sun cin ciyawa

Kano: Hotunan wani gidan azabtarwa da aka gano, an ceto maza da yara 47 da aka ɗaure da mari
Hoton wani da aka ceto a gidan azabtarwa a Kano. Hoto: BBC Pidgin
Source: Facebook

Sakamakon gano gidan azabtarwar, an kama wani Aminu Rabiu mai shekaru 35 da yayansa Fatihu Rabiu mai shekaru 40 da suka bude wurin ba bisa ka'ida ba duk da gwamnatin Kano ta haramta irin wannan gidajen tun watanni 10 da suka shude.

Kano: Hotunan wani gidan azabtarwa da aka gano, an ceto maza da yara 47 da aka ɗaure da mari
Hoton wasu maza da mari a kafarsu da aka ceto a gidan azabtarwa a Kano. Hoto: BBC Pidgin
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Irin wadannan gidajen azabtarwar da masu wurin ke kira 'cibiyoyin gyaran tarbiyya' sun dade kafin gwamnati ta haramta su bayan an gano cewa ana aikata munanan abubuwa da dama a wuraren.

Mene ke faruwa a cibiyoyin da gyaran tarbiyya?

A ruwayar na BBC Pidgin, wasu mutane da ke nema wa yaransu ko yan uwansu taimako saboda ta'amulli da miyagun kwayoyi ko wasu halayen marasa kyau sukan kai su cibiyoyin azabtarwan da nufin a musu magani.

Sai dai irin abubuwan da ake yi wa mutane a wadannan cibiyoyin sun hada da keta hakkin dan adam da cin mutunci.

Read also

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

Saboda irin wadannan abubuwan na keta hakkin ne jihohi da dama a arewa suka haramta irin wadannan gidajen na azabatarwa.

Yan sanda sun ce za su gurfanar da masu gidan a kotu idan sun kammala bincike tunda sun ki biyayya ga umurnin gwamnati na haramta irin gidajen azabtarwar.

Kano: Hotunan ɓarayin waya uku da aka kama bayan sun kashe wani sun ƙwace wayansa

A wani labarin, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama wasu mutane 3 da ake zargin sun sharba wa wani Mohammed Sulaiman wuka inda hakan ya kai ga ajalin sa sannan suka gudu da wayar sa.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, sun kara da bayyana cewa sun kai wa wani Kingsley farmaki a ranar Lahadi inda suka kwace wayar sa kuma suka tsere.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a wata takarda ta ranar Litinin, 20 ga watan Satumba ya ce sun kama wadanda ake zargin bisa laifin fashi da makami.

Read also

Zamfara na fama da 'yan gudun hijira 700,000, gidaje 3,000 sun halaka, Matawalle

Source: Legit.ng

Online view pixel