‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'ya'ya Mata 4 tare da mijinta

‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'ya'ya Mata 4 tare da mijinta

Aure abu ne mai kyau kuma waɗanda ke jin daɗin nasu na iya ba da shaidar hakan. A cikin 'yan shekarun nan, matan Najeriya suna ta samun soyayya a wajen kasarsu sannan suna ta auren fararen fata.

Legit.ng ta gabatar da matan Najeriya hudu da suka auri turawa.

1. Ireti ta auri masoyinta bature

Wata 'yar Najeriya mai suna Ireti ta auri kyakkyawar masoyinta bature mai suna Jesse, kuma kayatattun hotuna daga bikin aurensu sun haska kafofin sada zumunta.

A cikin kyawawan hotunan, Ireti da burin rayuwarta sun yi ado a cikin shiga ta al’ adar Yarbawa.

An taya masoyan murna a shafukan sada zumunta kuma mutane sun ce hotonan auren su ya nuna kyau da kasaita.

‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'Ya'ya Mata 4 tare da mijinta
‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'Ya'ya Mata 4 tare da mijinta Hoto: Naija Wedding
Source: Facebook

Read also

Haduwar Instagram ce: Kyakkyawar budurwa ta bayyana yadda ta samu mijin aure

2. Budurwa ta auri “abokin kasuwancin” saurayinta

Wata matashiya ‘yar Najeriya ta auri baturen da saurayinta mai zamba ya so damfara.

Saurayin ya nemi budurwar ta yi magana da baturen a madadinsa, amma labarin ya canza a hanya.

Bayan sun fada a kogin soyayyar junansu, Baturen ya zo Najeriya don ya auri budurwar a kotun ma’ aurata na Ikoyi.

‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'Ya'ya Mata 4 tare da mijinta
‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'Ya'ya Mata 4 tare da mijinta Hoto: @ijeomadaisy, @saintavenue_ent1
Source: Instagram

3. Remy ta fada soyayya da masoyinta bature

Bayan ta fada soyayyar baturen saurayinta, wata 'yar Najeriya mai suna Remy ta shiga daga ciki da dan kasar wajen.

Remy da abun kaunarta sun sanya kayan al’ ada iri guda yayin bikin aurensu kuma mutane da yawa sun taya su murnar aurensu.

‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'Ya'ya Mata 4 tare da mijinta
‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'Ya'ya Mata 4 tare da mijinta Hoto: @gossipmillnigeria
Source: Instagram

4. Yar Najeriya ta auri masoyinta bature

Wata mata 'yar Najeriya ta daura auren da masoyinta bature shekaru da suka gabata kuma kyakkyawan hoton iyalinsu ya kayatar da zukata lokacin da aka yada shi a kafafen sada zumunta.

Read also

Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta

Ma'aurata masu launin fata mabanbanta sun yi hoto tare da kyawawan 'ya'yansu mata guda hudu. Ma'auratan sun zauna kusa da juna yayin da mijin ya ɗauki yarsu ta ƙarshe a kan cinya inda sauran 'ya'yan uku suka tsaya a bayansu.

‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'Ya'ya Mata 4 tare da mijinta
‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'Ya'ya Mata 4 tare da mijinta Hoto: Asiyah Aisha Alubankudi
Source: Facebook

Bidiyon uwargida da ta fashe da kuka yayin da mijinta ya yi mata kyautar Venza tukwicin haifa masa ‘da

A gefe guda, wani bidiyo mai kayatarwa ya burge jama’a inda wata 'yar Najeriya ta fashe da hawayen farin ciki bayan mijinta ya yi mata kyautar mota kirar Vanza a matsayin tukwicin haifa masa ‘da namiji.

A bidiyon da @sikiru_akinola ya yada a shafin Instagram, an gano matar da mijinta suna rawa yayin da yayi mata jagora zuwa wajen motar.

A cewar @sikiru_akinola, kyautar ta zo kwanaki hudu bayan matar ta haifi ‘da namiji.

Source: Legit

Online view pixel