Gbajabiamila da 'yan siyasa 58 da suka kashe miliyoyi wurin ziyartar Tinubu

Gbajabiamila da 'yan siyasa 58 da suka kashe miliyoyi wurin ziyartar Tinubu

  • A kalla manyan 'yan siyasa da suka hada da masu rike da ofisoshin siyasa 58 ne suka ziyarci Bola Asiwaju Tinubu a London
  • Tun watanni uku da suka gabata jigon jam'iyyar mai mulki ya ke jinya bayan an yi masa aiki a guiwarsa a London
  • Tuni masoyansa, 'yan uwa, yaransa na siyasa, magoya baya da abokansa suka mayar da London tamkar wata Makka

A kalla jiga-jigan 'yan siyasa 58 tare da wadanda ke rike da ofisoshin siyasa a kasar nan suka kashe miliyoyin naira wurin kai wa jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Boka Tinubu ziyara a London, Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu jigon jam'iyya mai mulki ne wanda ya kwashe watanni uku a London ya na jinya. Makusancin tsohon gwamnan jihar Legas ya ce an yi masa aiki a guiwa kuma a halin yanzu likitocin kashi ne ke kula da shi.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

Gbajabiamila, gwamnoni da sauransu sun makure miliyoyin wurin ziyartar Tinubu
Gbajabiamila, gwamnoni da sauransu sun makure miliyoyin wurin ziyartar Tinubu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tun ranar 12 ga watan Augusta, yayin da shugaban kasa Muhammadu Burai ya ziyarcesa a London, yaransa na siyasa, masoyansa da magoya bayansu suka mayar da gidan tamkar filin arfa.

Sai dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai wa Tinubu Ziyara ne lokacin da ya je duba lafiyar kansa a birnin London din, Daily Trust ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya na daya daga cikin manyan 'yan APC da ke hararo kujerar shugabancin kasa. Duk da ana cece-kuce tare da maganganu kan cewa akwai wata rashin jituwa tsakaninsa da shugaban kasa Buhari kan batun shugabancin kasa a 2023.

Gwamnoni da suka ziyarcesa sun hada da Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi, Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu, Gwamnan Ogun Dapo Abiodun da Gwamna Umar Abdullahi Ganduje na jihar Kano wanda ya je UK domin shagalin kammala karatun dan sa.

Kara karanta wannan

Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna

Ganduje, dan sa Muhammad, 'yan majalisar jiharsa biyu, Kabiru Alhassan Rurum da Aminu Babba Dan Agundi sun ziyarci Tinubu.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya kai ziyara. A al'adance kuwa, kakakin majalisa ya na tafiya ne tare da wasu daga cikin hadimansa.

Kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa da dan majalisa James Faleke duk sun kai masa ziyara.

Bayan ziyarar da Sanwo-Olu ya kai masa, wasu wakilai da suka hada da mataimakin gwamnan jihar Legas, Obafemi Hamzat, shugaban ma'aikatan jihar, Tayo Ayinde, mataimakin shugaban ma'aikata, Gboyega Soyannwo da mai bada shawara na musamman kan harkar ilimi, Tokunbo Wahab duk sun je London.

Sauran sun hada da Sanata Tokunbo Abiru, Sanata Opeyemi Bamidele, Adeola Solomon, Adelere Oriolowo da Mohamed Sani.

Bayan kwanaki 37, Buhari ya yi shiru kan nadin sabbin ministoci daga Kano da Taraba

A wani labari na daban, kwanaki 37 bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fatattaki ministoci biyu, Sabo Nanono da Saleh Mamman kan rashin kwazo, har yanzu shiru ake ji.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Tun bayan sallamar ministocin biyu da aka yi a ranar 1 ga watan Satumba, manyan 'yan siyasan jihohin Kano da Taraba suna ta hango kujerun, Daily Trust ta ruwaito.

Duk da shugaban kasan ya sauya wa wasu ministoci ma'aikatu inda ya maye gurbin Nanono da Mamman, 'yan siyasan jami'iyyar mai mulki daga jihohin suke ta jajen tsaikon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel