Bayan kwanaki 37, Buhari ya yi shiru kan nadin sabbin ministoci daga Kano da Taraba
- Bayan kwanaki 37 da shugaba Buhari ya sallami Sabo Nanono da Saleh Mamman, har yanzu bai maye gurbinsu ba
- Hakan kuwa ya janyo ana ta hasashe inda ake hango Kawu Sumaila da Ismaeel Buba Ahmed daga Kano wurin maye gurbin Nanono
- A jihar Taraba kuwa, inda Saleh Mamman ya fito, a kalla 'yan jam'iyyar mai mulki 32 ke hango maye gurbinsa
Kwanaki 37 bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fatattaki ministoci biyu, Sabo Nanono da Saleh Mamman kan rashin kwazo, har yanzu shiru ake ji.
Tun bayan sallamar ministocin biyu da aka yi a ranar 1 ga watan Satumba, manyan 'yan siyasan jihohin Kano da Taraba suna ta hango kujerun, Daily Trust ta ruwaito.
Duk da shugaban kasan ya sauya wa wasu ministoci ma'aikatu inda ya maye gurbin Nanono da Mamman, 'yan siyasan jami'iyyar mai mulki daga jihohin suke ta jajen tsaikon.
Yayin da Kano ke da Bashir Magashi a matsayin ministan tsaro, Taraba ba ta da ko minista daya.
A Kano, tsohon hadimin shugaban kasa kan lamurran majalisar dattawa, Suleiman AbdulRahman wanda aka fi sani da Kawu Sumaila, da mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa, Ismaeel Buba Ahmed, tuni ake ta kallonsu a matsayin wadanda za su iya maye gurbin.
Sai dai, a kalla jiga-jigan jam'iyyar mai mulki 32 a jihar Taraba na rige-rige tare da fatan maye gurbin Mamman, Daily Trust ta wallafa.
Duk kokarin jin ta bakin shugabannin jam'iyyar na jihar Kano karkashin shugabancin Abdullahi Abbas domin tsokaci kan lamarin, ya gagara.
Sai dai wani bangaren jam'iyyar na jihar da tsohon shugaban kungiyar TBO, Alhaji Abdulmajid Danbilki Kwamanda, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta maye gurbin Nanono.
Ya yi bayanin cewa gurbin na jihar Kano ne kuma ya zama abun cece-kuce a jam'iyyar reshen jihar a wata daya da ya gabata saboda ba a sanar da mai maye gurbin Nanono ba.
Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu
A wani labari na daban, ana cigaba da matsanta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari lamba kan ya binciki daya daga cikin makusantansa, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da dukkan 'yan Najeriya da bincike ya bayyana sun adana kazamar dukiya a duniya.
Takardun Pandora da aka saki a wannan makon ya fallasa sirrin kazamar dukiyar wasu shugabannin duniya, 'yan siyasa da biloniyoyi da suka hada da masu fadi a ji a Najeriya.
Baya da Bagudu da Obi, akwai tsohon babban alkalin Najeriya, 'yan majalisa masu ci yanzu da tsoffin 'yan majalisa, fasto da kuma wasu manya a kasar nan da aka gano da hannu cikin satar kudade tare da boye kadarori a kasashen ketare.
Asali: Legit.ng