Shugabancin PDP: Tsaffin Gwamnonin Arewa 3 da Sanata 1 dake neman kujeran
- An kaddamar da yakin neman zaben kujeran shugabancin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP
- Akalla tsaffin gwamnonin daga Arewa uku ne suka bayyana aniyar neman wannan kujera
- Saboda haka, jigogin jam'iyyar na Arewa sun yi ganawar sirri a Abuja
Abuja - Yayinda jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party PDP ta shirya gudanar da taron gangaminta, tsaffin gwamnoni da tsohon Sanata sun bayyana niyyarsu na takaran kujeran.
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa yan takaran hudu sun bayyana niyyarsu ne da daren Alhamis, 7 ga Oktoba, bayan ganawar sirrin da jigogin jam'iyyar na Arewa sukayi a Abuja.
An tattaro cewa jigogin sun yi wannan ganawa ne domin hada kan yan Arewa.
An yi wannan ganawa ne a gidan hutun gwamnan jihar Bauchi dake unguwar Asokoro, Abuja, inda aka bayyanawa dukkan masu niyyar takara su bayyana da safiyar Juma'a, 8 ga Oktoba.
Sunayen wadanda ke da niyyar takara
Yan takaran daga yankin Arewacin Najeriya sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar, Ahmed Makarfi da kuma tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema.
Sauran sune tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo da kuma mataimakin jam'iyyar PDP, Sanata Suleiman Nazif.
A wani rahoton Thisday, dattawan Arewa na jam'iyyar sun fara da binciken wanda zai maye kujeran.
Sakamakon haka suka bada shawaran baiwa tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark ko Ibrahim Shema ko kuma tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.
Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba ya amince da karkatar da matsayin shugaban jam’iyyar zuwa Arewa.
Hukuncin ya biyo bayan amincewa da shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin karba-karba na babban taron jam’iyyar PDP na kasa wanda gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ke jagoranta.
Kwamitin karba-karba na Ugwuanyi ya musanya shugabanci da duk wasu mukamai na zababbun jam’iyyun da mutanen Arewa ke rike da su yanzu da na Kudu.
Kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan taron na NEC.
Asali: Legit.ng