Jerin jami'o'i 10 da aka fi daukan sabbin dalibai a Najeriya bana, Hukumar JAMB
Rahoto da hukumar shirya jarabawar shiga jami'a a Najeriya (JAMB) ta saki ya nuna jami'o'i goma da aka fi daukan sabbin dalibai a 2020.
A labarin da Premium Times ta koro, wadannan jami'o'i goma suka dauki kashi daya bisa biyar na daliban Najeriya da suka shiga jami'a a shekarar 2020.
Legit ta tattaro cewa daga cikin dalibai 551,553 da suka samu gurbin karatu a jami'oin Najeriya kawo watan Agusta, jami'o'in nan 10 sun dauki dalibai 101,034.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga jerin jami'o'in nan:
1. Jami'ar Ilori (UNILORIN) - Dalibai 13,634
2. Jami'ar Benin (UNIBEN) - 12,336
3. Jami'ar Maiduguri (UNIMAID) - 11,416
4. Jami'ar Calabar (UNICAL) - 10,888
5. Jami'ar Nnamdi Azikiwe (NAU) - 10,736
6. Jami'ar Port Harcourt (UNIPORT) - 9,509
7. Jami'ar Uyo (UNIUYO) - 8,502
8. Jami'ar Oye-Ekiti (FUOYE) - 8,110
9. Jami'ar jihar (EKSU) - 8,088
10. Jami'ar Lagos (UNILAG) - 7,815
Jerin jami'o'i 10 da dalibai suka fi nema a Najeriya, Hukumar JAMB
Wannan na kunshe cikin takardar rahoton hukumar da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya rattafa hannu.
Rahoton ya yi bayanin adadin daliban da suka nemi gurbin shiga kowace jami'a da kuma adadin makin da suka samu.
Ga jerin jami'o'in 10 da dalibai suka fi nema da adadin mutanen da suka nema:
1. Jami'ar Ilori (UNILORIN) - 78,466
2. Jami'ar Legas (UNILAG) - 59,190,
3. Jami'ar Benin, (UNIBEN) - 49,763;
4. Jami'ar Najeriya (UNN) - 47,239;
5. Federal University, Oye-Ekiti, 45,920;
6. Jami'ar Ahmadu Bello Zaria (ABU) - 44,509;
7. Jami'ar Bayeri Kano (BUK) 44,352;
8. Jami'ar Nnamdi Azikiwe - 43542;
9 Jami'ar Obafemi Awolowo - 42, 614
10. Jami'ar Jos (UNIJOS) - 38,309.
Asali: Legit.ng