Yanzu yanzu: Buhari ya gindaya sharuddan biyan albashin likitoci, ya soki yajin aiki
- Shugaba Muhammadu Buhari ya gindaya sharuddan biyan albashin likitoci da ke yajin aiki
- Buhari ya bayyana cewa har sai an gudanar da shirin tantancewa kafin a biya su kudaden da suke bi
- Ya kuma yi Allah-wadai da yajin aikin da likitocin da suka tafi a lokacin da 'yan kasar ke tsananin bukatarsu
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba za a biya kudaden da likitoci ke bi ba har sai an gudanar da shirin tantancewa.
Ya kuma ce za a sake nazarin alawus dinsu bayan an magance 'rarrabuwa mai zurfi tsakanin matsayin likitocin da ke yajin aiki'.
Shugaban kasar ya fadi hakan ne yayin wata ganawa da jami'an kungiyar likitocin Najeriya a fadar shugaban kasa, a cewar wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Garba Shehu ya fitar.
Buhari ya soki matakin kungiyar likitocin, yana mai cewa, 'Rayuwar ‘yan kasa da za a iya rasawa ko halaka a lokacin da likitoci suka janye ayyukansu, suna da daraja sosai da za a iya yin maslaha don warware sabani cikin lumana.'
Shugaban kasar ya kara da cewa:
“Bari in yi magana kai tsaye da likitocin da ke yajin aiki. Shiga yajin aiki a wannan lokacin da 'yan Najeriya ke matukar buƙatar ku ba shine matakin da ya dace a dauka ba, duk rintsi.
“Wannan Gwamnatin tana da kyakkyawan tarihi na biyan duk basussukan da ma’aikatan gwamnati, ‘yan fansho da ‘yan kwangila ke bi kuma har ma mun yi bitar basussukan da gwamnatocin baya suka bari, da zarar an kammala tantancewa. Za a warware basussukan da ma'aikatan lafiya ke bi.”
Na ga abubuwan da suka tabbatar da mutuncin Uzodinma, cewar Buhari yayin da ya kaddamar da ayyuka a Imo
Yajin aiki: FG ta ce babu likitan da ke bin ta ko naira daya
A baya mun kawo cewa, Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta musanta batun da ke cewa ta na rike da albashin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya inda ministan kwadago ya ce zancen kanzon kurege ne.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya bayyana hakan a wani taro na kwamitin gwamnatin tarayya a kan albashi tare da shugabannin kungiyoyin ma’aikatan lafiya.
Ngige ya ce, wadannan karairayin daga kungiyar likitoci masu neman kwarewa ne ta NARD, wadanda suke hana kowa ganin kokarin gwamnatin tarayya a kan harkar lafiya.
Asali: Legit.ng