Innalillahi: Hotunan yadda miyagun yan bindiga suka kai wani mummunan hari a jihar Zamfara

Innalillahi: Hotunan yadda miyagun yan bindiga suka kai wani mummunan hari a jihar Zamfara

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kuryar Madaro, dake yankin ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, jihar Zamfara
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe mutane da dama tare da ƙona gidaje da motoci
  • Wannan hari na zuwa ne bayan gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai cikinsu harda katse sabis a jihar

Zamfara - Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kuryar Madaro, ƙaramar hukumar Kauran Namoda, jihar Zamfara.

Rahoton BBC Hausa ya bayyana cewa mahara sun hallaka mutane da dama tare da ƙone gidajen mutane da motoci.

Wasu mazauna yankin sun tabbatar da cewa yan bindigan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 10:000 na dare, kuma sun ɗauki dogon lokaci suna cin karen su babu babbaka.

Harin jihar Zamfara
Innalillahi: Hotunan yadda miyagun yan bindiga suka kai wani mummunan hari a jihar Zamfara Hoto bbc.com/hausa
Asali: UGC

Hakazalika, maharan sun dibi kayayyakin abinci a shagunan yan kasuwa mazauna yankin da kuma dabbobi.

Kara karanta wannan

Hauka maganinta Allah: Wani mutumi ya hallaka matarsa mai kaunarsa da ɗan da suka haifa

Me jami'an tsaro suka ce game da harin?

Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta tabbatar da kai harin, amma ta bayyana cewa tuni aka tura jami'ai domin kai ɗauki.

Ƙauyen da yan bindigan suka kai harin yana ɗaya daga cikin yankunan da hukumomi a jihar Zamfara suka ɗauki matakin datse sabis da intanet.

Sai dai wasu mutanen kauyen da suka tsero zuwa Gusau, inda aka dage dokar datse sabis, sun bayyana cewa maharan sun kona gidaje aƙalla 13 da motoci 16.

Wasu hotuna da suka bazu sun nuna yadda aka cinnawa gidaje da motoci wuta a harin.

Hotuna daga Zamfara
Innalillahi: Hotunan yadda miyagun yan bindiga suka kai wani mummunan hari a jihar Zamfara Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Matakan da gwamnati ta ɗauka

Wannan na zuwa ne bayan ɗaukar tsauraran matakai da gwamnati ta yi domin magance ayyukan yan fashin daji a Zamfara.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa zuwa yanzun an kwashe fiye da wata ɗaya da ɗaukar matakan datse sabis, hana cin kasuwar mako-mako, hana saida fetur da sauransu.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 19, ciki har da ƙananun yara, sun ƙone shaguna da gidaje

A wani labarin na daban kuma Miyagu 30 sun mutu yayin da mayakan Ansaru da Yan bindiga suka fafata da juna a Kaduna

Wasu majiyoyi masu karfi sun nuna cewa ɓangarorin biyu sun fafata da juna ne a kokarin su na nuna karfin iko da yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Hassan Ibrahim, shugaban ƙaramar hukumar Birnin Gwari, ya bayyana cewa rikicin dake faruwa tsakanin waɗannan ɓangarorin biyu ya kawo raguwar satar mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262