Gwamnan PDP ya yi kusan shekara yana mulki shi kadai, babu Kwamishinoni a Gwamnati

Gwamnan PDP ya yi kusan shekara yana mulki shi kadai, babu Kwamishinoni a Gwamnati

  • Godwin Obaseki ya aika wa Majalisa sunayen kwamishinoni da zai yi aiki da su
  • Gwamnan na jihar Edo ya zabi kwamishinonin bayan watanni 10 da zarcewarsa
  • Obaseki ya zabi Crusoe Osagie da Esangbedo Ajose-Adeogun a matsayin hadimai

EdoJaridar Daily Trust tace watanni goma kenan da Godwin Obaseki ya koma kujerar gwamna a jihar Edo, amma har yanzu bai nada kwamishinoni ba.

A ranar Talata, 28 ga watan Satumba, 2021, aka samu labari cewa gwamna Godwin Obaseki, ya aika wa majalisar dokoki jerin sunayen kwamishinoninsa.

Takardar da gwamnan ya aika wa majalisa tana kunshe da sunayen mutane 11 da ake so a ba kujerar kwamishina, da kuma masu bada shawarwari biyu.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana ta hannun sakataren gwamnatin jihar, hadiman da aka zaba su ne; Crusoe Osagie da Sarah Esangbedo Ajose-Adeogun.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Crusoe Osagie zai rika mukamin mai bada shawara na musamman wajen ayyukan yada labarai, Ajose-Adeogun za ta taimaka wajen tsare-tsare da dabaru.

Gwamnan Edo
Gwamna Obaseki da Buhari Hoto: @GovernorObaseki
Source: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace Crusoe Osagie shi ne hadimin da ke taimaka wa wajen harkar yada labarai da dabarun sadar wa a lokacin gwamnatin Obaseki na farko.

Osarodion Ogie yace Ajose-Adeogun tsohuwar ma’aikaciyar Shell Petroleum Development Company ce.

Jerin Kwamishinonin da aka zaba

Kwamishinonin da gwamna Obaseki ya sake dawo wa da su, su ne; Monday Osagbovo, Marie Edeko, Misis Otse Momoh-Omorogbe da kuma Moses Agbukor.

Sauran wadanda aka aika wa majalisar dokokin jihar sunayensu su ne; Oluwole Osamudiamen Iyamu, SAN; Farfesa Obehi Akoria; da Dr. Joan Osa Oviawe.

Ragowar sun kunshi; Osaze Ethan Uzamere Joseph Eboigbe; Isoken Omo da Andrew Emwanta.

ASUU za ta zauna da Gwamnati

Kun samu labari cewa shugabannin kungiyar ASUU za suyi zama a makon nan da bangaren gwamnati. ASUU tana zargin gwamnati da saba alkawuran da ta yi.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Watanni 9 kenan da Gwamnatin Muhammadu Buhari tayi wa ASUU alkawari, amma ba ta cika ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel