Na fi zama cikin nishadi da farin ciki yayin da nake cikin fatara, Mawaki Akon

Na fi zama cikin nishadi da farin ciki yayin da nake cikin fatara, Mawaki Akon

  • Sanannen mawakin nan dan asalin kasar Senegal, Aliaune Damala Badara Akon Thiam, wanda aka fi sani da Akon ya ce ya fi farin ciki a cikin talauci
  • Fitaccen attajirin mawakin ya sanar da hakan ne yayin da ya ke tattaunawa da TMZ, wani shafin yanar gizo da kan tattauna da jama'a
  • Akon ya bayyana cewa, duk da nasarorinsa a rayuwa, a halin yanzu ya fi shan wuya tare da kokarin shawo kan matsalolinsa

Fitaccen mawakin duniya, ruwa biyu dan asalin kasar Senegal kuma baAmurke, Aliaune Damala Badara Akon Thiam, wanda aka fi sani da Akon, ya bayyana cewa ya fi zama cikin farin ciki yayin da ya ke talakansa.

Mawakin mai tarin nasara ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da yayi da fitacciyar shafin yanar gizo na TMZ, Daily Trust ta wallafa hakan.

Kara karanta wannan

Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

Na fi zama cikin nishadi da farin ciki yayin da nake cikin fatara, Mawaki Akon
Na fi zama cikin nishadi da farin ciki yayin da nake cikin fatara, Mawaki Akon. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin martani kan caccakar da aka yi masa kan fafutukar da masu kudi suke yi fiye da talakawa, Akon ya musanta cewa karuwar kudi na karo matsalolin rayuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya yi wannan tsokacin ne bayan fitaccen dan fim, Micheal K. Williams, ya rasu bayan dinkirar wasu magunguna da yayi.

Akon ya ce:

"Ba wai tuna baya ba ne, amma ina son bayyana cewa, wasu lokutan idan aka yi irin wannan tsokacin, ina yin martani ne daga irin abinda na fuskanta a rayuwa ta.
"Babu wanda zai zauna kuma ya sanar da ni cewa ban taba shiga fatara ba. A halin yanzu ina da matsalolin da na ke fama da su duk da nasarorin da na samu fiye da lokacin da na ke talaka. A gaskiya na fi walwala da farin ciki a lokacin da ba ni da komai."

Kara karanta wannan

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

Majalisa ta tabbatar da nadin wanda ya fara karatu tun ba a haife shi ba a cikin mashawartan EFCC

A wani labari na daban, a ranar Talata, majalisar dattawan Najeriya ta amince da nadin Yahaya Muhammad, a matsayin daya daga cikin mashawartan hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, wanda takardun sa suka nuna ya fara makarantar firamare da shekara daya kafin a haife shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Muhammad ya na daya daga cikin mutum biyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaba kuma majalisar ta aminta da su a ranar Talata.

Tabbatarwa tare da amincewa da wadanda Buhari ya zaba ya biyo bayan rahoton da kwamitin yaki da rashawa na majalisar, wanda Sanata Suleiman Abdu Kwari ke shugabanta ya mika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel