Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi

Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi

  • Mai kafar sada zumuntar Facebook, Mark Zuckerberg ya tafka mummunar asara daga dakatar da kafar na wasu sa’o’i
  • Ya yi asarar kimanin $6,000,000,000 yayin da ya yi gaggawar sauka kasa a cikin jerin masu kudin duniya ya koma kasan Bill Gates
  • Dama a ranar Litinin, 3 ga watan Oktoba ne kwatsam kafafen sada zumuntar zamani irin Facebook, WhatsApp da Instagram su ka dena aiki

Amurka - Wanda ya kirkiro kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Mark Zuckerberg ya tafka asarar fiye da $6,000,000,000 cikin sa’o’i kadan da dakatar da kafar, inda ya sauka kasa a jerin masu kudin duniya kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Lamarin da ya janyo asarar ta auku ne cikin sa’o’i kadan kwatsam kafafen sada zumuntar zamani kamar Facebook, Facebook Messenger, Instagram da WhatsApp su ka tsaya cak su ka dena yin aiki.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi
Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi. Hoto: Vangaurd NGR
Asali: Getty Images

Kamar yadda Yahoo Finance ta ruwaito, wannan lamarin da ya auku a ranar ranar Litinin 3 ga watan Oktoban 2021.

Dakatar da kafar ya janyo gabadaya dukiyar Zuckerberg ta sauka zuwa $121.6bn, yayin da ya sauka kasan Bill Gates inda ya koma na 5 a cikin jerin biloniyoyin duniya, ya sauka daga $140bn.

Dama Wall Street Journal ta fara wallafa akan illolin Facebook da sauran kafafe

A ranar 13 ga watan Satumba, Wall Street Jornal ta fara wallafa labarai akan yadda Facebook take sane akan illar da take yi wa yara mata masu karancin shekaru kamar yadda Instagram ma take yi.

Rahotannin sun janyo hankalin gwamnati kafin a wayi gari a ranar Litinin duk su ka dena aiki.

A wata tattauna da aka yi da Frances Haugen, tsohon ma’aikaciyar gyara akan ingancin Facebook, ta bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa Facebook ta san illar da take kawowa.

Kara karanta wannan

Tonon asiri: Yadda Stella Oduah ta wawuri N5b, ta siya katafaran gidaje a London

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, DW ta bayyana, kamfanin na sane da illar da take kawowa musamman ga yara kanana da suke amfani da Instagram wurin bayyana tsiraicin su, ga duniya.

Kamar yadda Haugen ta bayyana:

“Na ga irin illar da kafafen sada zumuntar zamani kamar Facebook suke haifarwa.”
“Irin Facebook din da ake yi yanzu ya na lalata mana yara kuma su na kawo illa ga dabi’u da al’adu a duniya.”

Sai dai a bangaren Facebook, sun bayyana cewa an dan samu wata matsala ne kuma kowa ya san za a iya samun irin wannan matsalar.

“Zai fi dacewa jama’a su fahimci cewa akwai yuwuwar a samu matsala da fasaha ko kuma wata ta daban,” kamar yadda Nick Clegg, mataimakin harkokin Facebook na duniya ya bayyana wa CNN.

Abin da yasa Abacha har abada zai cigaba da zama jarumi a jihar mu, Gwamnan PDP na Kudu

A wani labarin daban, Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba ya bayyana marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasa na mulkin soja a matsayin jarumi na jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Diri ya ce tsohon shugaban kasar ya samu wannan darajar ne saboda nan take da alkalami, marigayin, shekaru 25 da suka gabata (1996) ya kirkiri jihar ta Bayelsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnan na jihar Bayelsa ya mika godiyarsa ga marigayin shugaban wanda ya amince a kirkiri jihar da ke da kananan hukumomi takwas a lokacin wanda ya ce ya gaza adadin da kundin tsarin mulki ya tanada, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164