Zaben Anambra: IGP ya tura sabon kwamishina da dakaru na musamman

Zaben Anambra: IGP ya tura sabon kwamishina da dakaru na musamman

  • Hankula sun hadu waje daya don tabbatar da ganin cewa jihar Anambra tana cikin aminci da kwanciyar hankali gabanin zaben gwamnan ta
  • Hukumomin ‘yan sanda a kasar sun tura dakaru na musamman zuwa jihar ta kudu maso gabas gabanin fafatawar zaben
  • An kuma tura sabon shugaban 'yan sanda jihar domin sake fasalin tsarin tsaro da inganta shi

FCT, Abuja - Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba, ya ba da umarnin gaggauta tura Echeng Echeng a matsayin sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Anambra.

Echeng ya maye gurbin Tony Olofu, wanda aka sauya masa wajen aiki zuwa hedikwatar rundunar, Abuja, jaridar Punch ta ruwaito.

Zaben Anambra: IGP ya tura sabon kwamishina da dakaru na musamman
Zaben Anambra: IGP ya tura sabon kwamishina da dakaru na musamman Hoto: NPF
Asali: Facebook

Shugaban 'yan sandan ya kuma bayar da umurnin tura runduna ta musamman ta 'yan sanda don ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya da rundunar ke yi a Anambra.

Kara karanta wannan

Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba ta mai magana da yawun ‘yan sanda, Frank Mba, jaridar The Cable ta ruwaito.

Sanarwar ta ce:

“Sifeto Janar na 'yan sandan, IGP Usman Alkali Baba, psc (+), NPM, fdc ya ba da umarnin a gaggauta tura sabon kwamishinan 'yan sanda (CP) jihar Anambra.
“Sabon CP, Echeng Eworo Echeng, zai maye gurbin CP Tony Olofu wanda aka canza wa aiki zuwa hedikwatar rundunar, Abuja.
“IGP ya kuma ba da umarnin tura runduna ta musamman ta NPF zuwa jihar Anambra don karfafa gwiwa da kuma ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke yi na dawo da zaman lafiya a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

“IGP, wanda ya fi damuwa da sabbin hare-haren da aka kai kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Jihar, ya umarci sabon Kwamishinan ‘Yan sandan da ya yi amfani da doka da oda da kuma hanyoyin yaki da laifuka don kawar da mummunan halin da ake ciki, kwato wuraren jama'a daga 'yan daba da maido da zaman lafiya a jihar."

Sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taron jam'iyyar APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ya karbi wasu jiga-jigan siyasar jihar Anambra daga wasu jam'iyyu zuwa APC.

Ana ci gaba da yawaita sauya sheka a cikin wannan shekara, lamarin da ya kawo cece-kuce a jam'iyyun siyasa daban-daban na Najeriya.

Legit.ng Hausa ta lura cewa, akalla 'yan majalisa daga jihar Anambra 11 suka sauya sheka zuwa APC wanda gwamnan ya karbe su cikin lumana.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Asali: Legit.ng

Online view pixel