Dalilin da zai sa 'yan Najeriya su yi kewar Buhari bayan Mayu 2023 - Tsohon Minista

Dalilin da zai sa 'yan Najeriya su yi kewar Buhari bayan Mayu 2023 - Tsohon Minista

  • Tsohon Ministan Ilimi, Alhaji Yerima Abdullahi ya bayyana tarin hidimar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa kasar a karkashin mulkinsa
  • A cewar Abdullahi, miliyoyin 'yan Najeriya za su yi kewar shugabancin Buhari idan ya sauka a 2023
  • Ya ce masu halayya irin na shugaban kasar basu da yawa a cikin shugabannin Najeriya

Alhaji Yerima Abdullahi, tsohon Ministan Ilimi ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa kasar alheri kuma saboda haka da yawa daga cikin ‘yan Najeriya za su yi kewarsa lokacin da ya bar mulki a 2023.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa Abdullahi a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Gombe ranar Talata ya ce:

"Zan yi kewar Buhari bayan 2023 kuma akwai miliyoyin 'yan Najeriya da za su so, saboda idan ya ce fari ne, toh fari ne kuma idan ya ce baki ne, baki ne.

Kara karanta wannan

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

"Ko kuna son sa ko ba ku so, dole ne ku yarda cewa hakika Buhari ya yi wa kasar aiki mai kyau kuma ya sha wahala sosai wajen yi wa kasa hidima."
Dalilin da zai sa 'yan Najeriya su yi kewar Buhari bayan Mayu 2023 - Tsohon Minista
Dalilin da zai sa 'yan Najeriya su yi kewar Buhari bayan Mayu 2023 - Tsohon Minista Hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa Shugaban kasar yana da halayen jagoranci nagari wanda mafi yawan shugabannin Najeriya basu da shi musamman ganin irin tsayin daka da ya ke yi kan cin hanci da rashawa da kuma salon rayuwarsa abin koyi.

“Ba ku da irin waɗannan shugabanni da yawa a ƙasar. Shi ba ‘maradona’ ba ne; ba shi bane. Yana fadin abubuwa yadda suke. Yana da wuya ka sami shugaba mai irin wannan ƙarfin halin,” in ji shi.

Abdullahi ya ce gaskiyar Buhari ta taimaka wajen kafa harsashi mai karfi don ci gaban dimokuradiyya da shugabanci mai kyau a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Ya kara da cewa:

“Wadanda ke Allah wadai da Buhari ba wai suna yin hakan saboda baya kokari bane, suna yin hakan ne saboda shi Buhari ne.
“Yawancin wadanda ke yakar Buhari da gwamnatinsa suna yin hakan ne don kare kai. Akwai kuma wasu da suka dandani mulkinsa na soja kuma sun ƙi yarda cewa yanzu shi ɗan dimokuraɗiyya ne.
"Ba wai muna magana ne akan ‘yan tsirarun mutane bane illa a kan galibin talakawan Najeriya za su rasa halayen jagoranci na Shugaban kasar.
"Muna magana ne kan wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen sa na tallafi, manoma da ma wasu da dama wadanda suka ji tasirin kyakkyawan shugabanci a karkashin gwamnatinsa."

A cewarsa, Buhari ya yi wa kasa kokari sosai musamman wajen dawo da zaman lafiya da oda, ba tare da la’akari da abin da wasu ke tunani game da shi ba.

Rahoton ya kuma nuna cewa Abdullahi ya yaba da yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin da Buhari ke jagoranta, yana mai cewa an hukunta manyan mutane da yawa saboda cin hanci da rashawa a karkashin gwamnatin.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

"A karkashin Buhari, mun ga tsoffin gwamnoni, ministoci, sanatoci da aka yanke ma hukunci da aika su gidan yari kuma Shugaban kasar bai yafe masu ba," in ji shi.

Babu wani riba da Buhari ke samu, ba zai yarda da zango na uku ba - Yerima Abdullahi

A baya mun kawo cewa wani tsohon jakadan Najeriya a Malesiya a lokacin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo, Yerima Abdullahi, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba shi da sha'awar ci gaba da mulki har bayan 2023.

Abdullahi, ya ce Buhari yana yin “aikin da ba godiya” a matsayinsa na shugaban Najeriya, mai mutunta kundin tsarin mulki.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Punch a Gombe, a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel