Babu wani riba da Buhari ke samu, ba zai yarda da zango na uku ba - Yerima Abdullahi
- Yerima Abdullahi, tsohon jakadan Najeriya a Malesiya a lokacin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo ya magantu a kan batun zarcewar Shugaba Buhari a karo na uku
- Abdullahi ya bayyana cewa ya san Buhari ba zai taba yarda da sake zarcewa ba domin babu wani riba da yake samu
- Ya kuma kalubalanci mutane da su daina kokarin karkatar da hankalin shugaban kasar daga ayyukan gabansa
Wani tsohon jakadan Najeriya a Malesiya a lokacin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo, Yerima Abdullahi, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba shi da sha'awar ci gaba da mulki har bayan 2023.
Abdullahi, ya ce Buhari yana yin “aikin da ba godiya” a matsayinsa na shugaban Najeriya, mai mutunta kundin tsarin mulki.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Punch a Gombe, a ranar Laraba.
Abdullahi ya ci gaba da cewa
“Ya kamata mutane su zama masu gaskiya kuma su daina karkatar da hankalin shugaban kasar, tare fatan ganin ya mayar da hankali ga mayar da martani kan irin wadannan batutuwan.
"Na yi farin ciki da ganin cewa bai karkatar da hankalinsa ba. Shekaru biyu suka yiwa Buhari saura. Ya ce ba zai nemi wa'adi na uku ba. A'a, ba zan bukaci ya nemi karin wa'adi ba.
“Duk da haka, ko na nemi yayi haka ba zai so ba, na san shi sosai don haka na san ba zai so haka ba. Wani riba yake samu? ”
Tun da farko, jam’iyyar All Progressives Congress ta musanta ikirarin da jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, keyi na cewa shugaban kasar na shirin ci gaba da mulki.
Sakataren APC na rikon kwarya, Sanata John James Akpanudoehede, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja, ranar Laraba.
A wani labarin kuma, daya daga cikin manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya zauna da Channels TV, aka yi hira da shi game da Muhammadu Buhari da siyasar Najeriya.
Mista Segun Sowunmi ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba wani barazana ba ne ga jam’iyyar hamayya ta PDP a zabe mai zuwa na 2023.
“Buhari ba matsala ba ne, wannan karamin alhaki ne."
Asali: Legit.ng