Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta ware N100bn don zaben 2023

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta ware N100bn don zaben 2023

  • Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 100 domin gudanar da babban zaben kasar na 2023
  • Har ila yau, FG ta kara kasafin kudin kasa na shekarar daga naira tiriliyan 13.98 zuwa naira triliyan 16.45
  • Hakan na kunshe ne a cikin tsarin gyararren kasafin kudi na 2022-2024 na MTEF da shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Wakilai domin amincewa da shi

Gwamnatin tarayya ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan 100 domin gudanar da babban zaben shekarar 2023, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Haka kuma ta kara kasafin kudin kasa na shekarar daga naira tiriliyan 13.98 zuwa naira triliyan 16.45, wanda ke nuna cewa an samu karin tiriliyan 2.47, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta ware N100bn don zaben 2023
Gwamnatin tarayya ta ware N100bn don zaben 2023 Hoto: Femi Adsina
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin tsarin gyaran fuska na 2022-2024 na MTEF da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Wakilai don amincewa.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 30 ana bincike, an samu rigakafin ciwon zazzabin cizon sauro, Malariya

MTEF ya kasance na shekara-shekara, yana jujjuya tsarin kashe kudi na shekaru uku wanda ke ba da fifikon kashe kuɗi na matsakaicin lokaci da taƙaitaccen kasafin kuɗi wanda za a iya haɓaka tsare-tsaren bangare da tsaftace su.

Hakanan yana ƙunshe da ma'aunin sakamako don sanya ido kan kokarin bangare, Vanguard ta kuma ruwaito.

A tuna cewa a kwanakin baya ne majalisar ta zartar da na farko mai dauke da tiriliyan N13.98 na kasafin kudin kasa na 2022.

Amma a cikin wata wasika mai kwanan wata 2 ga Oktoba, 2021 da aka aika wa Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, Shugaba Buhari ya ce bukatar yin la’akari da sabbin sharuddan kasafin kudi a cikin Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA) 2021, da sauran muhimman kashe-kashe a cikin Kasafin Kudi na 2022 ya zama dole a sake nazarin MTEF.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Wannan ya zo ne yayin da Gbajabiamila ya yi fatali da duk wani yunkuri da wasu ‘yan majalisar suka yi a zauren majalisar na ranar Talata don ganin an yi muhawara kan kudirin kafin gabatar da kasafin kudin 2022 da Shugaban kasa zai yi a ranar Alhamis, tare da hana duk wasu abubuwan da ba a zata ba da za su iya dakatar da shi.

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 a ranar Alhamis ga majalisar dokoki

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 ga hadin gwiwar majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis mai zuwa, Vanguard ta ruwaito.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ovie Omo-Agege ne ya bayyana hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba a zauren majalisar dattawa da ke Abuja.

Ya sanar da hakan ne yayin da yake jagorantar zaman majalisar yayin da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, bai halarci taron ba.

Kara karanta wannan

Kocin Super Eagles, Gernot Rohr na bin albashin watanni 8, bashin N150m ya taru a kan NFF

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng