Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu

Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu

  • Ana cigaba da matsa wa shugaba Buhari kan ya binciki dukkan 'yan siyasa, masu kudi da shugabannin da bincike ya nuna sun saci kudin kasar nan
  • A cikin makon nan ne sakamakon gagarumin bincike da aka yi a duniya ya bayyana inda aka ga wasu 'yan siyasa, masu kudi, har da fasto da suka washe kudin kasar nan
  • Kungiyoyi masu zaman kansu sun cigaba da uzzura wa shugaban kasan da ya binciki duk wadanda aka fallasa, ganin matsayar gwamnatinsa kan yakar rashawa

Ana cigaba da matsanta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari lamba kan ya binciki daya daga cikin makusantansa, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da dukkan 'yan Najeriya da bincike ya bayyana sun adana kazamar dukiya a duniya.

Takardun Pandora da aka saki a wannan makon ya fallasa sirrin kazamar dukiyar wasu shugabannin duniya, 'yan siyasa da biloniyoyi da suka hada da masu fadi a ji a Najeriya.

Kara karanta wannan

Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu
Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Baya da Bagudu da Obi, akwai tsohon babban alkalin Najeriya, 'yan majalisa masu ci yanzu da tsoffin 'yan majalisa, fasto da kuma wasu manya a kasar nan da aka gano da hannu cikin satar kudade tare da boye kadarori a kasashen ketare.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki a kasar nan sun matsa wa Buhari lamba kan ya umarci hukumomin da suka dace da su binciki duk wadanda aka lissafo ganin irin matsayar mulkinsa kan rashawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Binciken da wata kungiyar 'yan jarida masu bincike na duniya suka yi, sun sanya wa aikin suna da aikin takardun Pandora.

Babu shakka aikin ya yi amfani da 'yan jarida 600 da kuma gidajen jaridu 150 a duniya da suka hada da jaridar Premium Times ta Najeriya kuma sun binciko takardun sirri kusan 11.9 miliyan wadanda suka fallasa asirin jama'a da yawa.

Kara karanta wannan

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Ku nemi EFCC da ma'aikatar sharia, cewar fadar shugaban kasa.

A yayin da Daily Trust ta bukaci jin ta bakin fadar shugaban kasa ta hannun babban mai bada shawara ta musamman ga shugaba Buhari kan yada labarai, Garba Shehu, ya ce:

"Kafin ku iso fadar shugaban kasa, zan shawarce ku da ku nemi EFCC da kuma ma'aikatar shari'a saboda su ke da alhaki.
"Muna jiran su bada shawara sannan mu san abun yi."

Kotu ta yi fatali da bukatar Ndume ta zare hannunsa daga shari'ar Maina

A wani labari na daban, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja a ranar Litinin ta yi watsi da bukatar da sanata Ali Ndume ya mika gabanta na son zare kan shi a matsayin tsayayyen Abdulrasheed Maina, bayan ya tsallake sharuddan beli.

Mai shari'a Okon Abang a hukuncin da ya yanke bayan bukatar da Ndume ya shigar gaban ta, ya ce hakan tamkar cin zarafin kotu ne ganin cewa ya mika irin wannan bukatar gaban kotun daukaka kara a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, ya tsallake beli bayan an sako shi daga gidan gyaran hali na Kuje inda ya kwashe kusan watanni 9 bayan an gurfanar da shi a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel