Da duminsa: Majalisar dattarwa ta tabbatar da sunaye 5 da Buhari ya aike mata a matsayin mambobin hukumar EFCC

Da duminsa: Majalisar dattarwa ta tabbatar da sunaye 5 da Buhari ya aike mata a matsayin mambobin hukumar EFCC

  • Majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen mutum biyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike mata don tabbatar da su a matsayin sakatare da mambobin Hukumar EFCC
  • Tabbatarwar ya biyo bayan samun rahoton kwamitin majalisar dattawa kan yaki da cin hanci da rashawa da laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa
  • A ranar Juma'a, 17 ga watan Satumba ne shugaban kasar ya aike da sunayen a cikin wata wasika inda ya nemi a gaggauta tabbatar da su

Majalisar dattawa a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, ta tabbatar da nade-naden da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a matsayin sakatare da mambobin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), jaridar The Nation ta ruwaito.

Wadanda aka tabbatar sun hada da George Abbah Ekpungu a matsayin Sakatare daga jihar Kuros Riba; Luqman Muhammed a matsayin mamba na hukumar daga jihar Edo; Anumba Adaeze a matsayin mamba daga jihar Enugu.

Read also

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Sai kuma Alhaji Kola Raheem Adesina shima a matsayin mamba daga jihar Kwara da kuma Alhaji Yahaya Muhammad a matsayin mamba daga jihar Yobe.

Da duminsa: Majalisar dattarwa ta tabbatar da sunaye 5 da Buhari ya aike mata a matsayin mambobin hukumar EFCC
Majalisar dattarwa ta tabbatar da sunaye 5 da Buhari ya aike mata a matsayin mambobin hukumar EFCC Hoto: Vanguard
Source: UGC

Tabbatarwar ya biyo bayan gabatarwa da kuma nazarin rahoton kwamitin majalisar dattawa kan yaki da cin hanci da rashawa da laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Kwamitin, Sanata Suleiman Abdu Kwari, a cikin rahotonsa, ya ba Majalisar Dattawan shawarar tabbatar da sunayen.

Bayan bayar da gudunmawa kan bukatar hukumar ta EFCC ta samu hukumar da za ta karfafa ayyukan hukumar, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege ya gabatar da rahoton sannan kuma aka aiwatar da shi, jaridar Daily Post ta ruwaito.

Jerin mutum 5 da Buhari ya nada a hukumar EFCC da sunayen jihohin da suka fito

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sakatare da mambobin kwamitin hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC).

Read also

'Yan bindiga sun kashe mutum 10, sun raunata wasu da dama a sabon harin da suka kai Katsina

Bukatar shugaba Buhari na tabbatar da nade-naden na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan wata Juma'a, 17 ga watan Satumba, kuma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, in ji jaridar The Nation.

A cikin wasikar, shugaban ya yi bayanin cewa bukatar tabbatar da wadanda aka zaba ta yi daidai da tanadin sashi na 2 (1) na dokar cin hanci da rashawa da ta’annati (Establishment) Act, 2004.

Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta tabbatar da wadanda aka nada a cikin “hanzari cikin sauri”.

Source: Legit.ng

Online view pixel