Jerin mutum 5 da Buhari ya nada a hukumar EFCC da sunayen jihohin da suka fito

Jerin mutum 5 da Buhari ya nada a hukumar EFCC da sunayen jihohin da suka fito

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumar yaki da yiwa tattalin arziki ta'annati (EFCC)
  • Legit.ng ta tattaro muku sunaye da jihohin jami'an biyar da majalisa ta tabbatar da nadinsu a yau
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya tabbatar da nadin na shugaba Buhari a shafinsa na Facebook

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sakatare da mambobin kwamitin hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC).

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa shugaban ya tura sunayen wadanda aka nada zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatarwa.

Bukatar shugaba Buhari na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan wata Juma'a, 17 ga watan Satumba, kuma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, in ji jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya aika wa 'Yan Majalisa takarda, ya yi sababbin nadin mukamai a EFCC

Jerin mutum 5 da Buhari ya nada a hukumar EFCC da sunayen jihohin da suka fito
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cikin wasikar, shugaban ya yi bayanin cewa bukatar tabbatar da wadanda aka zaba ta yi daidai da tanadin sashi na 2 (1) na dokar cin hanci da rashawa da ta’annati (Establishment) Act, 2004.

Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta tabbatar da wadanda aka nada a cikin “hanzari cikin sauri”.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, shi ma ya tabbatar da nadin shugaban a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sunaye da jihohin jami'an

Ga jerin jami'an da suka tsallake tantacewar zuwa matsayin da aka nada su:

  1. George Abang Ekpungu - Sakatare (Jihar Kuros Riba)
  2. Lukman Muhammed - (Jihar Edo)
  3. Anumba Adaeze - (Jihar Enugu)
  4. Alhaji Kola Raheem Adesina - (Jihar Kwara)
  5. Alhaji Yahaya Muhammad - (Jihar Yobe)

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

Majalisa ta nemi a bata rahoto kan kadarorin Janar Abacha da hankali zai dauka

Majalisar wakilai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ta nemi Kwamitin Aiwatarwa ta Shugaban Kasa (PIC) kan kadarorin da filaye mallakar gwamnati da su gabatar da rahotannin dukkan kadarorin da aka kwace daga tsoffin shugabannin Najeriya.

'Yan majalisar sun fi mayar da hankali musamman kan Janar Sani Abacha wanda Gwamnatin Najeriya ta kwato kaddarori da kudade da dama daga turai da aka ce mallakinsa ne, Daily Nigerian ta ruwaito.

Dan majalisar wakilai Ademorin Kuye, shugaban kwamitin wucin gadi kan kadarorin da aka yi watsi da su ya ce majalisar tana bukatar rahoton dukkan kadarorin da aka kwato daga hannun shugabanni, musamman Janar Abacha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.