Tonon asiri: Yadda Stella Oduah ta wawuri N5b, ta siya katafaran gidaje a London
- Bincike ya tattaro yadda Sanata Stella Oduah ta handami makuden kudi har N5 biliyan inda ta siya katafaren gidaje 7 a London
- Da sunanta ta siya gida daya, amma sauran shida ta yi amfani da dabarun su tare da kamfanoni ne wurin siya tare da boye su
- A tsakanin shekarar 2011 da 2014, an tsige ta a matsayin ministan sufurin jiragen sama sakamakon tsabar wawurar dukiyar kasa da ta ke yi
Takardun Pandora, daya daga cikin gagarumin binciken watanda da kazaman kudade da aka taba yi a duniya, ya fallasa Sanata Stella Oduah kan yadda a sirrance ta siya katafaren gidaje a London.
Kamar yadda binciken da wata gagarumar kungiyar 'yan jarida ta duniya ya bayyana, sama da 'yan jarida dari shida sun gano cewa wasu manyan gidaje 7 kadarorin Oduah ne da ke London, Daily Trust ta tattaro.
Daya daga cikin kadarorin an siya ne da sunanta, biyu kuwa da sunan kamfanonin Najeriya yayin da hudu daga cikinsu an siya da sunan kamfanin da ke boye mata dukiya na Seychelles.
International Trading and Logistics Company Limited (ITCL) an kafa shi ne a Seychelles, kamfanin da Oduah ta ke amfani da shi wurin bai wa dukiyar satar ta mafaka.
An gano cewa, ta yi amfani da kamfanin wurin siyan kadarori hudu a London masu darajar 6.7 million pounds tsakanin watan Oktoban 2012 zuwa watan Augustan 2013.
Ta yi aiki a matsayin ministan sufurin jiragen sama tsakanin shekarar 2011 da 2014 lokacin da aka fatattake ta sakamakon tsabar cin rashawar ta.
Kwamitin bincike biyu suka tuhumi Oduah inda aka tabbatar da cewa ta siya motoci biyu wadanda harsashi basu hudawa a karkashin hukumar kula da sufurin jiragen sama.
Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha
Gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi a halin yanzu ya zama abun magana kan dukiyar da ake zargin ya tara ta cikin dukiyar da Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasan Najeriya ya diba.
Akwai rahotanni kan yadda Bagudu ya dinga amfani da wasu kamfanoni wurin wawurar dukiya tare da hankada ta Turai amma gwamnan ya musanta, Daily Trust ta ruwaito.
A wani sabon sakamakon bincike mai suna Pandora Papers, daya daga cikin gagarumin bincike da aka taba yi na harkallar kudi a duniya, an bankado yadda ya tura wakilai Singapore domin neman masa mafaka ga abinda tsarin shari'ar Amurka ke neman kwacewa.
Asali: Legit.ng