Hotunan wani mutum da ya auri tukunyarsa ta dafa shinkafa ya ɗauki hankulan mutane

Hotunan wani mutum da ya auri tukunyarsa ta dafa shinkafa ya ɗauki hankulan mutane

  • Hotunan Khoirul Anam, dan kasar Indonesia da amaryar sa, wata tukunyar girkin lantarki ya janyo cece-kuce
  • Kamar yadda Anam ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya ce an daura auren su a ranar 20 ga watan Satumba
  • Hotunan sun bayyana shi sanye da fararen kaya na alfarma, tukunyar kuma lullube da mayafi irin na amare

Kasar Indonesia - Wani mutum dan asalin kasar Indonesia ya janyo cece-kuce bayan ya bayyana yadda shagalin auren sa da tukunyar girkin lantarkin sa ya kasance.

Kamar yadda ya wallafa hotunan bikin, ya na sanye ne da fararen kaya na alfarma yayin da tukunyar take lullube da mayafi irin na amare kamar yadda LIB ta ruwaito.

Hotunan auren wani mutum da tukunyar girkin lantarkinsa ya janyo cece-kuce
Hotunan auren wani mutum da tukunyar girkin lantarkinsa ya dauki hankula. Hoto: Khoirul Anam
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Hotunan auren wani mutum da tukunyar girkin lantarkinsa ya janyo cece-kuce
Khoirul Anam yayin da ya ke ratabba hannu kan takardar aure. Hoto: Khoirul Anam
Asali: Facebook

Anam ya kambama sabuwar amaryar ta sa

Mutumin mai suna Khoirul Anam cikin shauki da tsananin farin ciki ya yi wallafar ya na kambama amaryar ta sa inda ya sa “Sabuwar amarya”. Kamar yadda ya wallafa:

“Fara ce tas kuma ba ta da yawan magana ga shi ta kware a girki.”

Khoirul Anam ya wallafa hotunan a shafin sa na Facebook inda ya bayyana cewa an daura auren sa da tukunyar girkin lantarkin tun ranar 20 ga watan Satumba kamar yadda LIB ta ruwaito.

Hotunan sun yi yawo kwarai a kafafen sada zumuntar zamani inda mutane daban-daban su ka yi ta tsokaci iri-iri.

Hotunan auren wani mutum da tukunyar girkin lantarkinsa ya janyo cece-kuce
Ango Anam yayin da ya ke sumbatar amaryarsa tunkunyar girka shinkafa. Hoto: Khoirul Anam
Asali: Facebook

Hotunan auren wani mutum da tukunyar girkin lantarkinsa ya janyo cece-kuce
Ango Khoirul da amaryarsa tukunyar dafa shinkafa. Hoto: Khoirul Anam
Asali: Facebook

Ba Anam bane mutum na farko da ya auri abu mara rai a duniya ba.

Magidanci Ya Lakaɗa Wa Likitan Fata Mugun Duka Saboda Yaba Kyawun Fatar Matarsa

A wani labarin daban, 'yan sanda sun kama wani mutum bayan ya lakada wa likita dukan tsiya inda ya bar shi a mawuyacin hali bayan yabon kyawun fatar matar sa.

Kara karanta wannan

Shekarau ya ba Gwamnonin jihohin Kudu shawara, yace su daina barazana kan batun 2023

Matar wacce musulma ce mai sanye da hijabi ta sanar da mijinta, Bakhriddin Azimov cewa likitan fatar dan asalin kasar Rasha, Vladimir Zhirnokleev ya yaba kyawun fatarta.

Daga nan ne mutumin ya kai wa likitan farmaki, yanzu haka yana fuskantar hukunci akan cin zarafi kamar yadda LIB ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164