An cafke wani sojan karya da abokinsa da ke samar wa da 'yan bindiga hanyoyin sadarwa

An cafke wani sojan karya da abokinsa da ke samar wa da 'yan bindiga hanyoyin sadarwa

  • Jami'ain hukumar NDLEA sun yi nasarar cafke wasu mutane da ke kai wa 'yan bindiga abubuwan sadarwa
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihohi suka katse hanyoyin sadarwa a jihohinsu
  • An kama mutanen da wasu haramtattun abubuwan da suke da alaka da ta'addanci da barna

Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun cafke wani sojan karya, Hayatu Galadima da abokin aikin sa, Hamisu Adamu.

An bayyana cewa mutanen biyu suna kokarin shigar da muggan kwayoyi, alburusai da kayayyakin sadarwa ga 'yan bindiga a Kaduna lokacin da aka cafke su.

An cafke wani sojan karyada ke samar wa da 'yan bindiga hanyoyin sadarwa
Mutanen da aka kama | Hoto: NDLEA
Source: Facebook

Femi Babafemi, daraktan yada labarai na NDLEA, a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook na hukumar a ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a kan babbar hanyar Gwagwalada, Abuja.

Read also

Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

Abubuwan da aka kwato a hannunsa

An kwato wasu abubuwa daga mutanen biyu. Daga cikinsu akwai; harsasai 21 na RLA masu girman 7.45mm da aka boye a cikin kwalbar ruwa, fakiti 16 na sabbin rediyon sadarwa (Walkie talkie) da kuma abin rufe kai mai launin soji guda hudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashin sanarwar na cewa:

"Yayin da Hayatu Galadima ya yi ikirarin cewa shi Lance Kofur ne da ke aiki a Ibadan, sun kara da cewa suna kai haramtattun abubuwan ne zuwa Kaduna da Kano. Binciken farko duk da haka yana nuna cewa wadanda ake zargin na iya kasancewa da alaka tsakaninsu da 'yan bindiga a Arewa maso Yamma."

Ku tuna cewa an dakatar da ayyukan sadarwa a jihohin Zamfara, Sokoto da Kaduna kwanan nan.

A cewar Babafemi, akwai yiyuwar wadanda ake zargin na jigilar radiyon sadarwar ne ga 'yan bindigan da dakatarwar ta shafa.

Read also

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Kwamandan FCT na hukumar da ya yi kamen an umurce shi da a mika wadanda ake zargi ga hukumomin da abin ya shafa don ci gaba da bincike.

Hukumomin da aka ambata sune Sojojin Najeriya da wata hukumar leken asiri, wacce tun farko ta sanya mutanen biyun a cikin jerin wadanda ta ke nema.

An cafke kasurgumin kwamandan 'yan bindigan da ya addabi jihar Zamfara

A bangare guda, Ayuba Elkanah, kwamishinan 'yan sanda a Zamfara, ya ce rundunar 'yan sanda ta cafke wani kasurgumin kwamandan 'yan bindiga mai suna Bello Rugga, The Cable ta ruwaito.

Elkanah ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake gabatar da wanda ake zargi kwamanda ne tare da wasu mutane 21 da ake zargi da fashi da makami a Gusau.

Ya ce an kashe wasu 'yan bindiga biyar yayin wani samame da suka kai a karamar hukumar Gummi ta jihar.

Read also

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Source: Legit.ng

Online view pixel