COAS ga sojoji: Kada ku daga kafa wajen ragargazar 'yan ta'adda

COAS ga sojoji: Kada ku daga kafa wajen ragargazar 'yan ta'adda

  • Shugaban hafsun soji ya bukaci sojoji da su ci gaba da aiki tukutu don yakar ta'addanci
  • Janar Farukh Yahaya ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai a jihar Nasarawa
  • Ya kuma gargadi sojoji da su kasance masu jajircewa da nuna kwarewa wajen gudanar da ayyukansu

Nasarawa - Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Farouk Yahaya ya umarci runduna ta bataliya ta 4 ta musamman da ke Doma da su ci gaba da jajircewa don ganin sun kubutar da kasar daga hannun mayakan Boko Haram da sauran 'yan ta'adda a Arewa da sauran sassan kasar.

Yahaya ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake zantawa da Daily Trust yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar bataliyar da ke karamar Hukumar Doma ta Jihar Nasarawa don duba wasu wurare a barikin.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Ya ce kalubalen tsaro da ke fuskantar kasar nan ba za a iya shawo kansu ba idan aka babu kulawa da jajircewa daga gwamnatin tarayya.

COAS ga sojoji: Kada ku daga kafa wajen ragargazar 'yan ta'adda
Shugaban hafsun soji, Farukh Yahaya | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

COAS, duk da haka, ya gargadi sojojin da su kasance ko yaushe masu nuna kwarewar aiki da ladabi da hazaka wajen gudanar da ayyukansu na tsaron kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ziyarci babban basaraken gargajiya na yankin, Andoma na Doma, Alhaji Aliyu Onawo Ogah, inda ya bukaci cibiyoyin gargajiya da su yi aiki tare da hukumomin tsaro a jihar.

Andoma na Doma, Alhaji Aliyu Onawo Ogah, ya ce ziyarar ta zo a kan lokaci domin hakan zai karawa mutane kwarin gwiwa kan yaki da laifuka da rashin tsaro.

Sheikh Gumi ga 'yan Arewa: Hanyoyin da za ku zauna lafiya da 'yan bindiga

A bangare guda, Babban malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, ya shawarci mutanen yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da ta’addanci kan yadda za su zauna lafiya tare da ‘yan bindigar da ke mamaye dazuzzukan su.

Kara karanta wannan

A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

Malam Gumi ya ce mutane za su iya habaka "alakar juna da 'yan bindiga ba tare da an cutar da su ba", PRNigeria ta ruwaito

An nakalto malamin yana fadi yayin da yake gabatar da lacca a jami'ar ABU da ke Zariya a ranar Alhamis cewa:

“Alakar da nake da ita da 'yan bindiga ta kasance mai sauki saboda ko yaushe ina ‘shiga wurinsu.”

'Yan sanda sun cafke tsageru 13 da ake zargi 'yan bindiga ne kuma barayin shanu a Katsina

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar atsina ta cafke mutane 13 da ake zargi da hannu a fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da safarar makamai da kuma ta’addancin kan 'yan jihar da ba su ji ba su gani ba.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Katsina, Gambo Isah ne ya bayyana hakan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Mista Isah ya ce kamun wadanda ake zargin ya kasance wani bangare na nasarorin da rundunar 'yan sandan jihar ta samu a baya-bayan nan a ci gaba da yaki da miyagun laifuka da aikata laifuka a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.