Da Ɗuminsa: 'Yan bindiga sun ƙona mutum 10 da ransu, sun yi wa wasu 15 yankan rago a Jihar Niger
- Yan bindiga sun afka wasu garuruwa a jihar Niger sun tafka mummunan ta'addi
- Yan bindigan sun kona mutum 10 da ransu, sun yanka wasu sannan sun sace mata
- James Jagaba, sakataren karamar hukumar Munya ya magantu kan mummunan harin
Jihar Niger - Wasu mutane da makamai da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kona mutane 10 da ransu a garin Kachiwe da ka mazabar Sarkin Pawa a karamar hukumar Munya na jihar Niger.
Yan bindigan sun kuma sace mutane bakwai yayin harin kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton na SaharaReporters ya ce sakataren karamar hukumar Munya na jihar, James Jagaba ya bada labarin abin da ya faru wanda ya kira 'mummunan lamari.'
Ya kara da cewa yan bindigan sun kuma tafi kauyen Shape a mazabar Sarkin Pawa inda suka yi wa mutum tara yankan rago yayin da sauran mutane suka tsere, ya kara da cewa sun kuma kashe mutum 7 a Gogope.
Ya ce:
"Yan bindigan sun kona gidaje da dama, sun kona mutum 10 da ransu, sun sace mata bakwai sun yanka wasu. A hanyarsu ta zuwa aikata mummunan aikin, sun hadu da mutane biyu da abin hawarsu ya lalace, sun tsaya sun kashe su sannan suka kona motarsu. Yayin hakan, mata uku da suka sace suka tsere amma sun tafi da sauran bakwai.
"Yan bindigan sun tashi kowa a garin, babu wanda ya sha. Mun san abin da ya faru ne ta bakin mata ukun da suka tsere kuma har yanzu ba su cikin hayacinsu."
Mazauna kauyen ba su iya kiran jami'an tsaro ba saboda toshe layin sadarwa
An gano cewa yan bindigan na cin karensu ba babbaka saboda toshe hanyoyin sadarwa da aka yi da ya shafi sassan wasu garuruwan.
James ya ce:
"An fada mana an yi kokarin sanar da jami'an tsaro amma hakan bai yi wu ba saboda babu layin sadarwa na karamar hukumar Manya tsawon kwanaki. Mutanen ba su samu ikon sanar da jami'an tsaro ba ko karamar hukuma. A karamar hukumar, sakon bai zo mana da wuri ba don haka ba mu iya samun jami'an tsaro ba."
Ban Taɓa Sanin Garkuwa Da Mutane Laifi Bane Har Sai Da Hukuma Ta Damƙe Ni, Shugaban Ƴan Bindiga, Surajo Mamman
A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani jagoran ‘yan bindiga wanda da kan shi ya bayyana yadda ya halaka kuma ya yi garkuwa da mutane da dama kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.
Dan bindigan, Surajo Mamman wanda aka fi sani da ‘Kutaku’ mai shekaru 50 da haihuwa ya bayyana cewa shi ne na biyu daga Sani Muhidinge, dan bindigan da gwamnati take nema ido rufe.
ahinde ya boye ne a dajin Rugu dake tsakanin jihar Katsina da jihar Zamfara. Jami’an tsaro sun tafi da shi har hedkwatar ‘yan sanda a ranar Laraba a gaban manema labarai.
Asali: Legit.ng