A tsaka da rade-radin sauya sheka, tsohon shugaban kasa Jonathan ya gabatar da muhimmiyar bukata gabannin 2023

A tsaka da rade-radin sauya sheka, tsohon shugaban kasa Jonathan ya gabatar da muhimmiyar bukata gabannin 2023

  • Gabanin babban zaben 2023, tsohon shugaban kasa Jonathan ya bukaci ‘yan majalisu da su ba da damar watsa sakamakon zabe ta na’ura
  • Tsohon Shugaban kasar ya bayyana cewa watsa sakamakon ta na’ura zai tabbatar da akwai gaskiya yayin da za a kaucewa rikicin zabe
  • Majalisar kasa na gab da aikewa da kudirin dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima ga Shugaba Buhari don amincewa

FCT, Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta ba da damar amfani da na’ura wajen watsa sakamakon kafin 2023.

Premium Times ta ruwaito cewa Jonathan ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba, yayin da yake gabatar da lacca a bikin kaddamar da Kwalejin Tsaron Kasa, a Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

A tsaka da rade-radin sauya sheka, tsohon shugaban kasa Jonathan ya gabatar da muhimmiyar bukata gabannin 2023
A tsaka da rade-radin sauya sheka, tsohon shugaban kasa Jonathan ya gabatar da muhimmiyar bukata gabannin 2023 Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Babban tanadi mai cike da cece-kuce a cikin kudirin shine Sashe na 52, wanda ke magana game da watsa sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura.

Jonathan ya bukaci 'yan majalisar da su ba da damar watsa sakamakon zabe ta hanyar na’ura don nuna gaskiya da kuma kaucewa rikici, jaridar The Cable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin da ake ciki, Majalisar Dokoki ta kasa ta kafa wani kwamiti don ganawa da warware sabanin da ke cikin kudurin dokar zabe da Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka zartar a watan Yuli.

Sanatocin APC sun ki amincewa da tura sakamakon zabe ta na'ura

A wani labari, mambobin Jam’iyyar APC a majalisar dattijai a ranar Alhamis sun kada kuri’ar kin amincewa da aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura.

Kwamitin Majalisar a cikin rahotonsa ya ba da shawarar a Sashe na 52 (3) cewa, INEC “na iya tura sakamakon zabe ta hanyar na’ura in akwai damar yin hakan.”

Kara karanta wannan

‘Yan IPOB sun kashe tsohon Sarki, Mijin tsohuwar Minista da Direban ‘Dan Majalisa a wata daya

Amma wani sanatan APC daga Jihar Neja ta Arewa, Sabi Abdullahi, ya gyara ayar dokar zuwa, “INEC na iya yin la’akari da tattara sakamakon zabe ta na’ura mai kwakwalwa, in har aka yi la’akari da cewa tsarin sadarwar na kasa ya kai gwadaben da Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta aminta da shi kuma Majalisar Tarayya ta amince da hakan.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng