'Yan IPOB ne suka kashe mijin tsohuwar minista Dora Akunyili, tsohon jigon IPOB
- Wani tsohon jigo a haramtacciyar kungiyar IPOB ya bayyana IPOB a matsayin 'yan ta'adda
- Ya bayyana cewa, 'yan IPOB ne suka kashe mijin marigayiya tsohuwar minista Dora Akunyili
- Ya kuma ce, dukkan wasu kashe-kashe a yankin 'yan IPOB ne suke aikatawa cikin rashin tausayi
Uche Mefor, barrantaccen mataimakin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, ya zargi kungiyar da kisan Dakta Chike Akunyili a jihar Anambra, ShaharaReporters ta ruwaito.
Dakta Chike shine mijin marigayi Dora Akunyili, tsohuwar Ministar Yada Labarai da Sadarwa kuma Darakta-Janar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC).
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun harbe Dakta a ranar Talata 28 ga watan Satumba yayin da yake dawowa Enugu daga Onitsha, inda ya halarci lacca na tunawa da aka shirya don girmama marigayiyar matarsa.
Kwanan nan, an yi kashe-kashe a yankin Kudu Maso Gabas da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka aikata.
Gwamnati da wasu mutane na zargin haramtacciyar kungiyar IPOB da reshen mayakan ta wato ESN da hannu a kashe-kashen, zargin da kungiyar ta IPOB ta sha musantawa.
Kisan na Dakta Chike na da alaka da 'yan kungiyar IPOB wanda shugabansu ke tsare a hannun gwamnatin tarayya, amma kungiyar ta karyata, inda ta ce kisan nasa na da alaka da 'yan siyasa.
Da yake mayar da martani kan kisan gillar da aka yi wa Akunyili, Mefor ta shafinsa na Facebook a ranar Alhamis 30 ga watan Satumba ya zargi IPOB da karkacewa daga "gwagwarmayar 'yanci" zuwa kisan 'yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba.
Da yake tabbatar da irin barnar aikin ta'addanci na IPOB, Mefor ya ce, IPOB ne ke da alhakin kashe-kashe a yankin ciki har da:
“Na baya-bayan nan shine kisan gilla da aka yiwa Dr Akunyili."
Ya kuma bayyana babban abin kunya ne ga manya a yankin kudu maso gabas su gagara ambatan sunan 'yan IPOB a matsyain 'yan ta'addan da suke aikata munanan kashe-kashe a yankin.
Gwamna ya sanya N20m ga duk wanda ke da bayanai kan kashe mijin Dora Akunyili
Gwamna Willie Obiano ya sanar da ba da ladar Naira miliyan 20 ga duk wanda ke da bayanai masu amfani da za su kai ga cafke wadanda ke da hannu a kisan gillar Dakta Chike Akunyili da sauran munanan hare-hare a jihar Anambra.
A yau ne aka tashi da labari mara dadi da ke cewa, wasu 'yan bindiga sun harbe Dakta Chike Akunyili, mijin wata jigo a gwamnatin baya, Dora Akunyili.
Gwamnan na Anambra ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba.
Obiano ya koka kan yadda wasu 'yan ta'adda dauke da makamai suka kaddamar da ta’addanci tare da kai hare-hare kan ‘yan kasa a sassa daban-daban na jihar a cikin 'yan kwanakin da suka gabata.
Wani mahaifi ya kashe dansa mai shekaru 2 da tsananin duka da bulala
Wani mutum mai suna Vwede ya lakadawa dansa mai shekaru biyu duka har lahira a Yenagoa, jihar Bayelsa kuma ya tsere, The Nation ta ruwaito.
Lamarin, wanda ya faru ranar Lahadi 26 ga watan Satumba a kan titin Imiringi a Yenagoa, ya jawo Allah wadai daga makwabta da masu rajin kare hakkin dan adam.
An tattaro cewa mahaifin da ake zargi, daga jihar Delta, ya yi wa yaron mai shekaru biyu bulala mai tsanani sannan ya kai shi asibiti a kan hanyar Ruthmore Hotel a Immiringi bayan yaron ya suma.
Asali: Legit.ng