COVID-19: Shugaba Buhari ya killace kansa, fadar shugaban kasa ta bayyana dalili

COVID-19: Shugaba Buhari ya killace kansa, fadar shugaban kasa ta bayyana dalili

  • Bayan shafe sati daya a New York, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya tare da mukarrabansa
  • Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana dalilin da ya sa Buhari da mukarrabansa suka fara killace kansu bayan tafiyar
  • Keɓewar kwanaki 5 da Shugaban kasar ya shiga ya yi daidai da ƙa'idodin Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC)

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara killace kansa bayan dawowarsa daga taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na 76 daidai da ka’idojin tafiye-tafiye na COVID-19.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya tabbatar wa PM News ci gaban a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

COVID-19: Shugaba Buhari ya killace kansa, fadar shugaban kasa ta bayyana dalili
COVID-19: Shugaba Buhari ya killace kansa, fadar shugaban kasa ta bayyana dalili Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

A cewar Adesina, shugaban kasar da hadiman da suka yi masa rakiya zuwa Amurka sun shiga killace kansu tun bayan dawowar su a ranar Lahadi, 26 ga Satumba.

An bayyana hakan ne bayan rashin bayyanar Buhari a taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ci gaba da cewa Buhari zai gama killace kansa a ranar Alhamis, 30 ga watan Satumba.

Hotunan dawowar Buhari daga US, ya taho da ayyuka na musamman daga UN

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan kwashe mako daya ya na ayyuka a taro karo na 76 na majalisar dinkin duniya a birnin New York da ke Amurka.

Newswire ta ruwaito cewa, shugaban Najeriyan ya dawo da bukata na musamman daga sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, wurin tabbatar da daidaituwar siyasar kasashen yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

Guterres, wanda ya yabi Buhari kan yadda ya ke shugabanci a Afrika tare da kawo daidaito a yankin, ya zanta tare da shugaban kasar Najeriyan a taron UNGA kashi na 76, Newswire ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng