Hotunan dawowar Buhari daga US, ya taho da ayyuka na musamman daga UN
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira birnin Abuja bayan halartar taron gagarumin UNGA karo na 76
- Antonio Guterres, sakataren majalisar dinkin duniya ya bai wa Buhari babban aiki idan ya iso gida
- Ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da dawowar daidaituwar shugabanci a kasashen Afrika ta yamma
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan kwashe mako daya ya na ayyuka a taro karo na 76 na majalisar dinkin duniya a birnin New York da ke Amurka.
Newswire ta ruwaito cewa, shugaban Najeriyan ya dawo da bukata na musamman daga sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, wurin tabbatar da daidaituwar siyasar kasashen yammacin Afrika.
Guterres, wanda ya yabi Buhari kan yadda ya ke shugabanci a Afrika tare da kawo daidaito a yankin, ya zanta tare da shugaban kasar Najeriyan a taron UNGA kashi na 76, Newswire ta ruwaito.
Majalisar dinkin duniya ta gano cewa nahiyar Afrika, ballantana Afrika ta yamma a da ta kasance wurin da shugabanci na gari ya samu wurin zama, amma cikin kwanakin nan ta kasance cikin wani hali sakamakon juyin mulkin da ake ta fuskanta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai
A wani labari na daban, a abinda da ya janyo wa hukuma NYSC cece-kuce, ta aminta da cewa daga cikin takardun bayanai kan tsaronta ne ga ma'aikata da kuma 'yan bautar kasa aka samu wannan shawarar wacce ta matukar tada kura.
Shawarar ta bukaci duk masu hidimar kasa da kuma ma'aikata masu kaiwa da kawowa kan manyan tituna da ke da hatsari da su sanar da iyaye, 'yan uwa da abokan arziki ko kuma wadanda za su iya biyan kudin fansarsu idan an sace su.
Hukumar ta ce ta gaano cewa tabbas wannan takardar ta gama yawo a gari amma akwai wadanda babu wannan shawarar a ciki, Premium Times ta wallafa.
Asali: Legit.ng