Gangamin taron jam'iyyar APC na jihohi: Gwamna Ganduje ya yi magana kan jihar Kano

Gangamin taron jam'iyyar APC na jihohi: Gwamna Ganduje ya yi magana kan jihar Kano

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya bayyana cewa a halin yanzun suna jiran a rantsar da shugabannin kananan hukumomi na APC
  • Ganduje ya kuma bayyana cewa jiharsa ta kammala shirin gudanar da gangamin taron APC na jiha, wanda ke tafe
  • Hakanan kuma ya umarci dukkan muƙarrabansa da su halarci wurin taron bikin murnar ranar samun yancin kai ranar Jumu'a

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yace jiharsa ta shirya wa babban taron APC na jihohi, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Ganduje yace:

"Mun shirya wa gamgamin taron jam'iyyar APC na jihohi da za'a gudanar ranar 16 ga watan Oktoba, 2021."
Ganduje yace Kano ta shirya
Gangamin taron jam'iyyar APC na jihohi: Gwamna Ganduje ya yi magana kan jihar Kano Hoto: pulse.ng
Source: UGC

Gwamnan ya faɗi haka ne a wurin taron majalisar zartarwa na gwamnatinsa, jim kaɗan kafin a fara taron, wanda ya gudana a gidan gwamnati, ranar Talata.

Read also

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

"Mun kamala taron gundumomi, haka kuma an gudanar da na ƙananan hukumomi daga baya. Bayan rantsar da shugabannin gundumomi, yanzun muna jiran a rantsar da na kananan hukumomi."
"Mun shirya zuwan taron APC na jihohi, mun kammala duk wasu shirye-shirye da ake bukata wajen gudanar da shi a jihar mu."

Kowa ya halarci faretin ranar yanci -Ganduje

Ganduje ya umarci kwamishinonin jihar da mashawarta su halarci taron fareti na musamman ranar samun yancin kai mai zuwa, 1 ga watan Oktoba.

Ganduje ya ƙara da cewa:

"Kwamishinan yaɗa labarai ne zai jagoranci kwamitin shirya bikin murnar zagayowar ranar samun yancin kan Najeriya."
"Ina umartan dukkan kwamishinoni da masu bada shawara da su halarci wurin ranar Jumu'a, inda za'a yi fareti na musamman."

A wani labarin na daban kuma Gwarazan yan sanda sun cafke wani mai garkuwa da mutane a Kano

Read also

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

Jami'an yan sanda sun samu nasarar damƙe wani mutumi da ake zargin ɗan garkuwa ne a ƙaramar hukumar Tsanyawa, jihar Kano.

Mutumin mai suna, Tukur Ahmed, ya shiga hannu ne biyo bayan barazanar da ya yi wa wani cewa zai sace shi ko ƴaƴansa idan bai biya miliyan N1m ba.

Source: Legit

Online view pixel