Da Dumi-Dumi: Kotu ta tsige dan majalisar tarayya na jam'iyyar APC daga kujerararsa
- Wata kotun tarayya dake zamanta a Jalingo, jihar Taraba, ta tsige ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bali/Gasol, Hon. Mubarak Gembo
- Kotun ta umarci INEC ta kwace shaidar zaɓe daga hannun tsohon ɗan majalisar ta baiwa wanda bincike ya gano shine ya taka takara
- Lauyan wanda aka tsige, ya bayyana cewa zasu jira matakin da uban gidansu zai ɗauka kan hukuncin kotun
Taraba - Babbar kotun tarayya dake zamanta a Jalingo, babban birnin jihar Taraya, ta tsige ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Bali/Gasol, Hon. Mubarak Gembo, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Alkalin kotun, mai shari'a Simon Amonbita, ya umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta kwace shaidar zaɓe da ta baiwa ɗan majalisar cikin gaggawa.
Alkalin ya bayyana cewa matuƙar ɗan takara bai cike ƙa'idojin da matakan zabe ba, bai dace a bashi satifiket ɗin tabbatar da nasarar zaɓe ba, kamar yadda ya faru da Gambo.
Hakanan kuma kotun ta umarci Honorabul Gambo, na jam'iyyar APC, ya daina nuna kansa a matsayin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Bali/Gasol.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kotu ta umarce shi ya dawo da albashin da ya karɓa
Mai shari'a Amonbita, ya umarci Gambo, ya maida kuɗaɗen da ya karba tun sanda aka rantsar da shi a matsayin mamba a majalisar wakilai tun da ya yi amfani da yaudara wajen shiga ofis.
Daga nan kuma kotun ta umarci INEC ta baiwa, Garba Hamanjurde, shaidar zaɓe, kasancewar shine ya taka takara kuma ya cike dukkan sharuɗɗan zaɓe a mazaɓar Bali/Gasol.
Zamu jira ɗaukar matakin Honorabul Gambo - Lauya
Da yake martani kan hukuncin, lauyan Mubarak Gambo, wanda aka tsige, Festus Idekpefor (SAN), yace zasu jira matakin da uban gidansu zai ɗauka.
A nasa ɓangaren, Garba Hamanjurde, yace ɓangaren shari'a ya ƙara tabbatar da sahihancinsa, kuma zai jira ya ga an aiwatar da hukuncin na kotu.
A wani labarin na daban kuma Wani Matashi Dan Shekara 25 Ya Hallaka Mahaifiyarsa Saboda Abinci
Rundunar yan sanda reshen jihar Oyo, ta gurfanar da wani matashi ɗan shekara 25, Solomon, bisa zargin kashe mahaifiyarsa.
Rahoton yan sanda ya nuna cewa wanda ake zargin ya tura mahaifiyar tasa ne cikin rijiya saboda tace masa babu abinci a gida.
Asali: Legit.ng