Innalillahi: Wani Matashi Dan Shekara 25 Ya Hallaka Mahaifiyarsa Saboda Abinci
- Rundunar yan sanda reshen jihar Oyo, ta gurfanar da wani matashi ɗan shekara 25, Solomon, bisa zargin kashe mahaifiyarsa
- Rahoton yan sanda ya nuna cewa wanda ake zargin ya tura mahaifiyar tasa ne cikin rijiya saboda tace masa babu abinci a gida
- Jami'an yan sanda sun samu nasarar kama wanda ake zargin ne bayan samun rahoto daga yan uwansa
Oyo - Rundunar yan sanda reshen jihar Oyo, ta gurfanar da wani matashi ɗan kimanin shekara 25 a duniya, Solomon Ochadi, a gaban kotun majistire dake zamanta a Ibadan, bisa zarginsa da hallaka mahaifiyarsa, Elizabeth Ochadi.
Punch ta rahoto cewa rundunar yan sandan ta gurfanar da manomin matashin ne kan zargi ɗaya tal, na kisan kai.
Karamin sufetan yan sanda, mai gabatar da ƙara, Opeyemi Olagunju, ya faɗa wa kotun cewa wanda ake zargin ya ingiza mahaifiyar tasa ne cikin rijiya.
Yace hakan ya yi sanadiyyar mutuwar matar yar kimanin shekara 50, wacce take uwa a gare shi, a cikin rijiya.
Meyasa ya tura mahaifiyarsa cikin rijiya?
Da yake labartawa kotu yadda lamarin ya faru, mai gabatar da ƙara na rundunar yan sanda yace wanda ake zargin ya nemi abincinsa daga mahaifiyar tasa bayan ya dawo daga gona.
Yace:
"Matar ta shaida masa cewa babu abinci a gidan. Ba zato sai ya ingizata cikin rijiya saboda fushi da amsar da ta ba shi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta."
Bayan kasheta, su waye suka tona asirinsa?
Olagunju, ya cigaba da shaidawa kotu cewa bayan ya kashe ta, Solomon ya nemi wuri a bayan gidansu ya yi wa gawarta ƙabari.
Kannen matashin, da suka ganewa idonsu abinda ya faru, sune suka sanar da yan sanda, kuma aka cafke wanda ake zargin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wane mataki kotu ta ɗauka?
Majistire Olaide Hamzat, yace kotu ba ta da hurumin yanke hukunci kai tsaye, domin akwai bukatar a gudanar da bincike.
Bisa haka ne ya bada umarnin a kai fayil da kuma shaidu zuwa hukumar zartar da hukunci domin shawarwari kuma ya ɗage zaman zuwa 23 ga watan Nuwamba.
A wani labarin na daban kuma Dan majalisar wakilan tarayya ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki
Wani ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Benuwai ya bayyana sauya shekarsa daga Labour Party (LP) zuwa APC mai mulki.
Godday Samuel Odagboyi, mai wakiltar Apa/Agatu yace ya ɗaukiɓwannan matakin ne saboda rikicin cikin gida da ya addabi LP.
Asali: Legit.ng