PDP ta caccaki gwamna, mataimakiyarsa da kakakin majalisa bisa barin jama'arsu don tare wa a kasar waje

PDP ta caccaki gwamna, mataimakiyarsa da kakakin majalisa bisa barin jama'arsu don tare wa a kasar waje

  • A halin yanzu, da alama babu kowa a kasa wanda zai yi aiki a matsayin shugaban gwamnatin jihar Ogun
  • Wannan ya kasance ne saboda gwamnan jihar, mataimakiyarsa, da kakakin majalisar ba sa Najeriya
  • Gwamna Dapo Abiodun da Noimot Salako-Oyedele suna Burtaniya yayin da kakakin majalisar, Olakunle Oluomo, ke Amurka

Da take Allah wadai da wannan, PDP reshen Ogun ta ce wannan shine babban rashin sanin yakamata a harkokin mulki

Rashin kasancewar Gwamna Dapo Abiodun, mataimakinsa, Noimot Salako-Oyedele, da kakakin majalisar dokokin Ogun, Olakunle Oluomo, a jihar na haifar da damuwa sosai a jihar.

PDP ta caccaki gwamna, mataimakiyarsa da kakakin majalisa bisa barin jama'arsu don tare wa a kasar waje
PDP ta caccaki gwamna, mataimakiyarsa da kakakin majalisa bisa barin jama'arsu don tare wa a kasar waje Hoto: Ogun State House of Assembly
Source: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Abiodun ya bar kasar zuwa Burtaniya don kai ziyarar ban girma ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kwanan nan yayin da Salako-Oyedele ke London.

Bugu da kari, an ce Oluomo yana Amurka don taron kasa da kasa.

Read also

Da Dumi-Dumi: Sanata tare da dubbannin mambobin PDP sun sauya sheka zuwa APC mai mulki

Wannan gibi da aka samu a manyan kujeru uku na jihar ya haifar da tsoro, tashin hankali, da zafin martani daga mutane da yawa.

Jaridar ta kuma rahoto cewa a nata bangaren, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana lamarin a matsayin "karshen rashin sanin ya kamata a harkokin mulki."

Wannan shi ne jawabin shugaban jam’iyyar PDP na Ogun, Sikirulahi Ogundele, wanda ya zanta da manema labarai kan lamarin mai tayar da hankali.

Ogundele ya ce:

“Gwamna ya yi tafiya, mataimakinsa da kakakin majalisa sun bi shi; gaskiya, ban yi takaici ba tunda ba su da alkibla tunda ba su da hangen nesa. Ban ji takaici ba.
"Za a fara bikin ranar 'yancin kai na shekara-shekara a ranar Juma'a, kawai su koma jihar Ogun su yi bikin ranar."

Read also

Hotunan shugaban EFCC yayin da ya gurfana a gaban kotu domin bada shaida

A wani labari na daban, gabanin bikin cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a rufe wasu sassan sakatariyarta da ke Abuja.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa anyi hakan ne a wani bangare na kokarin tabbatar da bikin samun 'yancin kai a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba cikin nasara.

Legit.ng ta tattaro cewa ginin sakatariyar yana kusa da dandalin Eagles Square kuma cewa za a gudanar da babban taro na 'yancin kai a ranar Juma'a a wajen.

Source: Legit.ng

Online view pixel