Bikin 'yancin kai: FG ta tsaurara matakan tsaro, za ta rufe sakatariya a ranar Alhamis 30 ga wata
- Gwamnatin tarayya ta ce za a rufe wasu sassan sakatariyarta a ranar Alhamis 30 ga watan Satumba
- Folashade Yemi-Esan, Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, ta ce hakan zai ba da damar kiyaye oda kafin bikin cika shekaru 61 da samun 'yancin kai
- Yemi-Esan ta bayyana cewa an shirya wasu tsare-tsare don bikin a dandalin Eagles a ranar Juma'a, 1 ga Oktoba
FCT, Abuja - Gabanin bikin cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a rufe wasu sassan sakatariyarta da ke Abuja.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa anyi hakan ne a wani bangare na kokarin tabbatar da bikin samun 'yancin kai a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba cikin nasara.
Legit.ng ta tattaro cewa ginin sakatariyar yana kusa da dandalin Eagles Square kuma cewa za a gudanar da babban taro na 'yancin kai a ranar Juma'a a wajen.
Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci manyan jami’an gwamnati da abokan kasar zuwa wurin taron.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saboda dalilan tsaro ne
An tattaro cewa shirin rufe katafaren ginin da ke kallon dandalin saboda tsaro ne.
A cewar rahoton, Folashade Yemi-Esan, Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, ta bayyana matakin da gwamnatin ta dauka a cikin sanarwa.
An bayar da rahoton cewa sakataren din-din-din, ofishin jin dadin hidima na OHCSF, Ngozi Onwudiwe, ne ya rattaba hannu kan wasikar, kuma an aika ta ne ga dukkan ministoci, shugabannin hukumomi, shugabannin kwamitoci, sakatarori na dindindin da sauran su.
Jaridar Vanguard ta kuma ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta fadakar da jama'a don kara tsaurara matakan tsaro a shirye -shiryen bikin cika shekaru 61 da samun 'yancin kasar.
Wannan gargadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a Abuja.
Majalisar dokoki ta tsaurara matakan tsaro kan wata zanga-zangar ma'aikata
A gefe guda, wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar na nuni da cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Majalisar Dokoki ta kasa domin dakile wata zanga-zangar da wasu masu taimaka wa majalisar suka shirya.
Majalisar a safiyar ranar Litinin, Litinin, 27 ga watan Satumba, ta tsaurara matakan tsaro bayan ma’aikata karkashin kulawar ma’aikatan majalissar suka tunzura don gudanar da zanga-zanga kan batun albashinsu.
Jami'an tsaro da suka hada da masu kwantar da tarzoma da 'yan sanda na yau da kullum, ma'aikatan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran jami'an tsaron majalisa duk hallara don kula da hanyoyin shiga da fita daban-daban a harabar majalisar.
Asali: Legit.ng