Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumomin ICPC, RMAFC

Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumomin ICPC, RMAFC

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a hukumomin ICPC da RMAFC
  • A hukumar yaki da cin hanci da rashawa, shugaban kasar ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da kwamishinoni biyar da za su cike guraben ayyuka
  • Hakazalika Buhari ya nemi a tabbatar da wani wanda aka zaba a matsayin Kwamishinan Tarayya na Hukumar tattara kudaden shiga (RMAFC)

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da kwamishinoni biyar da za su cike guraben ayyuka a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Ya kuma bukaci Majalisar Tarayyar da ta tabbatar da wani wanda aka zaba a matsayin Kwamishinan Tarayya na Hukumar tattara kudaden shiga (RMAFC).

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa buƙatun shugaban kasar na ƙunshe ne a cikin wasiƙu biyu mabanbanta da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Shugaba Buhari a daya daga cikin wasikun ya bayyana cewa bukatarsa ta tabbatar da wadanda ya zaba a hukumar ICPC ya yi daidai da tanadin sashe na 3 (6) na Dokar Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka makamanta, 2000.

Wadanda aka zaba don mukamin a ICPC sun hada da:

1. Dr. Mojisola Yaya-Kolade, Ekiti (Kudu maso Yamma)

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Misis Anne Otelafu Odey, Cross River (Kudu maso Kudu)

3. Alhaji Goni Ali Gujba, Yobe (Arewa maso Gabas)

4. Dr. Louis Solomon Mandama, Adamawa (Arewa maso Gabas)

5. Sanata Anthony O. Agbo, Ebonyi (Kudu maso Gabas).

A wani lamari makamancin haka, Buhari a wata wasika ta biyu ya nemi Babban Majalisar ta tabbatar da nadin Engr. Mohammed Sanni Baba a matsayin Kwamishinan Tarayya na Hukumar tattara kudaden shiga, mai wakiltar Jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Jagoran kungiyar yakin neman zaben Tinubu na kasa ya ajiye aiki

A cewar Shugaban kasar, an gabatar da bukatar tabbatar da wanda aka zaba ne bisa tanadin sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin 1999 na Tarayyar Najeriya (kamar yadda aka yi wa gyara).

Bikin 'yancin kai: FG ta tsaurara matakan tsaro, za ta rufe sakatariya a ranar Alhamis 30 ga wata

A wani labari na daban, mun ji cewa gabanin bikin cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a rufe wasu sassan sakatariyarta da ke Abuja.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa anyi hakan ne a wani bangare na kokarin tabbatar da bikin samun 'yancin kai a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba cikin nasara.

Legit.ng ta tattaro cewa ginin sakatariyar yana kusa da dandalin Eagles Square kuma cewa za a gudanar da babban taro na 'yancin kai a ranar Juma'a a wajen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel